Wata mata da ta bayyana cewa ta jima tana soyayya da danta, ta kara da cewa yanzu haka suna shirin aure.
Wani abin mamaki ga soyayyar ta su shine, matar mai suna Betty Mbereko wadda 'yar asakin garin Mwenezi a jihar Masvingo, yanzu haka tana dauke da cikin wata shida, wanda dan nata ya yi mata.
Idan matar ta haihu dan zai kasance da ko jika kenan?
Matar ta kai tsawon shekaru 12 ba tare da miji ba, inda take tare da danta, Farai Mbereko mai shekaru 23.
Majiyar ta rwaito cewa matar ta kudiri aniyar auren dan cikin nata ne maimakon ta auri kanin mijinta. Sannan kuma ta kara da cewa ta soma soyayya da dan nata ne shekaru uku da suka gabata.
Matar ta ce ta kashe makudan kudade wajen daukar nauyin karatun dan nata, bayan da mijinta ya rasu, inda ta ce bayan Farai ya kammala karatu ya samu aiki, babu macen da ta dace ta more shi kamarta.
Title :
Wata Uwa Na Shirin Auren Danta A Kasar Zimbabuwe
Description : Wata mata da ta bayyana cewa ta jima tana soyayya da danta, ta kara da cewa yanzu haka suna shirin aure. Wani abin mamaki ga soyayyar ta s...
Rating :
5