DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Wata Baiwar Allah mai suna Hajiya Ramatu Tijjani, ta yi asubanci inda ta halarci unguwar Kiristoci ta Sabon Tasha dake Kaduna, sannan ba ta zame ko'ina ba sai a Babban Cocin dake Unguwar, inda ta halarci bauta da addu'o'i na Kiristocin, bayan an kammala ne ta mika kyautar Littattafan Bible har guda 50, ga Limamin Cocin.
Hajiya Ramatu Tijjani wacce ta iso Cocin tare da wani danta mai suna Abdul Hakeem, ta samu kyakkyawar tarba daga Matan Zumunta na Cocin, inda suka rungumi juna suna zubar da hawaye.
Hajiya Ramatu Tijjani wacce ta koka dangane da yadda son zuciya da mugunta suka bata kyakkwar dangatakar dake tsakani Kiristoci da Musulmai musanmam a jihar kaduna, inda ta dora laifin akan miyagun Malamai na bangarorin biyu.
Baiwar Allah Ramatu ta kara da cewar, hikimar bayar da wadannan Litattafai na Bible ga Kiristocin ba domin komai bane, saidai domin kara dankon zumunci a tsakanin Musulmai da Kiristocin wadanda aka raba kawunansu.
Ramatu Tijjani ta bayyana cewar ta sani wasu zasu iya sukanta dangane da abinda tayi, inda tace wannan baya damunta ko kadan, domin ta tabbatar ita Musulma ce, babu wanda ya isa ya koreta daga musulunci, sannan bazatayi nadamar abinda tayi ba.
Lokacin da yake maida jawabi na godiya, Limamin Cocin Pastor Yohanna Buru, ya zubar da kwalla akan abinda ya gani, inda yayi fatan wannan zumunci zai cigaba da dorewa tsakanin al'ummar Musulmi da Kirista a fadin jihar.
Pastor Buru wanda jama'a ke yi wa lakabi da Najashin wannan zamani sakamakon alakar sa da Musulmai, ya ce a kowace ranar Lahadi ana samun Musulmai dake halartar Cocin nasa, domin gudanar da Sujada tare da sauran Kiristoci, wanda wannan kyakkyawar ci gaba ne inji shi.
Title :
Wata Mata Musulma Ta Bayar Da Gudummuwar Littattafan Bible 50 Ga Kiristoci A Kaduna
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Wata Baiwar Allah mai suna Hajiya Ramatu Tijjani, ta yi asubanci inda ta halarci unguwar Kiristoci ta Sabon Ta...
Rating :
5