A wani hoton bidiyo mai tsawon mintuna uku da ya bayyana a kwanan nan, an nuna yadda wata jami'ar soja take ta lakadawa wani matashi duka saboda ya ce mata kyakkyawa.
A bidiyon, an nuna yadda matar take ta jibgarsa tare da korafin cewa 'ni za ka kalla ka cewa kyakkyawa? Lallai ka raina min hankali. Kuma sai na yi maganin ka".
Haka kuma an nuno wasu daga cikin abokan aikinta maza da mata suna taya ta dukansa.
A gefe daya kuma, cibiyar makarantar sojoji ta NDA, ta nuna rashin jin dadinta kan abin da dalibar sojar ta yi, inda suka bayyana cewa suna kan gudanar da bincike. Sannan kuma sun gano cewa lamarin ya auku ne a shekarar 2014 a wani yanki a jihar Lagos.
Title :
Wata Jami'ar Sojan Nijeriya Ta Lakadawa Wani Matsashi Duka Saboda Ya Ce Mata 'Kyakkyawa'
Description : A wani hoton bidiyo mai tsawon mintuna uku da ya bayyana a kwanan nan, an nuna yadda wata jami'ar soja take ta lakadawa wani matashi du...
Rating :
5