Mazauna kauyukan Mairi da Malari sun yi hijira zuwa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno sakamakon farmakin da 'yan Boko Haram suka kai kauyukansu.
Bincike ya nuna cewa 'yan bindidan sun kai farmaki kauyukan ne a daren ranar Juma'a, inda suka kashe mutane hudu tare da kona kauyukan baki daya.
Kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana, an kai harin na kauyen Mairi ne da misalin karfe takwas na dare, inda aka kashe wani yaro da kuma mata guda uku, kafin daga bisani auka kara gaba zuwa Malari inda suka bankawa kauyen wuta, yayin da su kuma mazauna kauyan suka gudu.
Wani mazaunin yankin mai suna Moduu Idirissa ya bayyanawa manema labarai cewa yaron da 'yan bindigan suka kashe malami ne a wata makarantar Islamiyya.
Ya kuma kara da cewa su kuma mata guda ukun sun gamu da ajalinsu ne sakamakon gazawa wajen cetar da rayuwarsu a yayin da aka bankawa gidajensu wuta.
A yayin da majiyarmu ta ziyarci kauyen a jiya, ta bayyana cewa ta ga dubban mazaunan kauyukan suna ta yin hijira zuwa garin Maiduguri dauke da kayansu a kai.
Title :
Wasu Mazauna Kauyukan Jihar Borno Sun Yi Hijira Sakamakon Harin Boko Haram
Description : Mazauna kauyukan Mairi da Malari sun yi hijira zuwa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno sakamakon farmakin da 'yan Boko Haram suk...
Rating :
5