Daga Umar Bandi Kofar Kware
Gaisuwa mai yawa, tare da girmamawa, ina mai cike da farin cikin samun nasarar da ka yi, domin ka ceto kasar nan daga halin da ta sami kanta, wani abin jin dadi tare da yi wa Allah godiya, ka dauki matakan da suka dace, wadanda ka jima kana nanatawa, cewa sune suka yima ci gaban wannan kasa da bai-bayi ta ko wace huska, da suka hada da matsalar tsaro, wannan matsala ga dukkanin alamu zata zama tarihi, disa ga matakan da ka dauka na zakulo zaratan kwamdoji da hafsoshin Soja masu tsananin kishin kasa da son zaman lafiya da karuwar arziki, wannan abin ayaba ne, ga wannan tsarin wanda yaba jama’ar da suka gudu suka bar garuruwansu na asali a yau suka dawo har suyi bacci su hantse.
Ba wannan ne kawai ba, ya zama dalilin da gabatar ma, da wannan ‘yar gajeruwar wasika, wannan ya biyan ababe biyu zuwa uku, da suka hada matakin da ka dauka domin dakile duk wata kafa da marasa kishin kasa da al’umma suke bi, suna yin sama da fadi da dukiyar kasa wadda aka basu amana, wannan matakin yayiwa ‘yan kasa da dama dadi, wanda yafi musu dadi yadda ake zakulo wadanda suka wawushe kudaden sayen makamai, wadanda suka nuna rashin tausayi da tausayawa, wadanda ake kisa a tsakanin Sojoji da fararen hulla da akewa yankan raga akwashe musu dukiya a kona gidajensu, lamarin da ya zama dalilin wadanda suka tsira da rayukkansu yin hijira zuwa wadansu kasashe.
Wani abin haushi da takaici, ga wadanda suka wata kansu da asusun ajiyar ‘ya ‘yansu, da faduwar jam’iyyar PDP yazo musu ba tsammani, wanda da tayi nasarar lashe zabe, da ba’a sanin irin wannan barna da yaudara da sukawa al’ummar kasar nan, na tabbata kana son ganin Najeriya ta koma akan hayyacinta, da kimarta da mutuncin al’ummar ta a idanun duniya, musamman yadda sunan kasar ya baci tayi fice akan cin hanci da rashawa, wannan yaki na cin hanci da karbar rashawa, yana da matukar bukatar, ya sami hadinkai da goyon bayan bangaren shara’a, wanda ya zama wajibi ayiwa wannan sashe gyara, yadda doka kan iya hawan duk wanda ya takata.
Amma lamarin na bukatar kashe masa makuddan kudade, da zai hana sashen ga karbar rashawa, tare da samar da hukumce-hukumce masu tsanani ga wanda aka sama da haka, idan aka dauki irin wadannan mataki, zai iya kai manufar taka ga samun nasara, wasu jama’a suna bayyana haushi da takaici akan dokar nan mai lamba 308 wadda ta hana shugaban kasa da mataimakinsa, gwamna da mataimakinsa gurfana a gaban Kotu, duk laifin cin amanar kasar da sukayi, wannan sashen yana bukatar gyra domin a tanadi wani hukumcin da zai cilasta duk gwamnan da aka sama da sama da fadi da kudaden al’umma, doka ta dakatar dashi da mataimakinsa, abaiwa kakin majalisar dokoki ta jihar riko.
Hakika irin matakan da aka dauka, akan matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya, matsalace wadda a babba, wadda itace ta zama ginshikin samar da kowane irin koma baya a kasar nan, ‘yan kalilan ke sarafa dukiyar kasa yadda suke so, miliyoyi na mutuwa akan curuta da rashin wadataccen abin sawa bakinsu, jama’a da dama suna cike da farin ciki, akan yadda ake bankado wadanda sukayi rubdaciki da kudaden al’umma, sai dai wani hanzari ba guduba, duk da cewa kasha fada tare da nanatawa kana sane da irin halin matsin da jama’a, suke ciki wanda suna neman mafita.
Allah ya karamaka lafiya da yawancin rai mai albarka, bunkasa Noma yana daya daga cikin manufofin gwamnatinka, tun kamin ka sami nasarar zama shugaban kasa, akan burinka na kasar ta daina dogaro da albarkatun danyen mai, wanda farashinsa ya fadi kasa war-wars, shi kansa wannan sashen da ya sami nasara da samun minista masani akan noma kuma mai kishi yana da muhimmancin gaske, yadda ka zakulo hafsoshin Soja ka danka musu amanar kawo karshen ‘yan boko Haram har abin na neman ya zama tarihi, shi kansa Noman yana da matsayi da kimar da zaka zakulo kwararu masu amana da ciki da wajen kasar ka daka musu amanar wannan sashen, nasan kasani amma ina tunatar da kai cewa, talakawa a kasar suna cikin wani hali na samun hauhawar farashin kaya, adalilin tashin
Title :
Wasika Zuwa Ga Shugaban Kasa Najeriya
Description : Daga Umar Bandi Kofar Kware Gaisuwa mai yawa, tare da girmamawa, ina mai cike da farin cikin samun nasarar da ka yi, domin ka ceto kasar...
Rating :
5