Daya daga cikin manyan hafsan sojojin Sama da ake zargi da karbar wasu kaso daga cikin dala milyab 2.1 na kudin sayen makamai wanda ke tsare a barikin Niger dake Abuja, ya maido da naira milyan 66 cikin milyan 90 din da hukumar EFCC ke zargin ya karba.
Sakamakon haka ne aka saki hafsan sojan, sannan kuma aka umarce shi da ya je ya nemo cikon kudin da ya rage, wato naira milyan talatin.
Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyana cewa hakan ba wai na nufin an kammala tuhumar da ake yi masa ba ne.
Bincike ya nuna cewa sauran manyan hafsoshon sojojin da ofishin sojojin sama ke tsare da su a madadin hukumar EFCC, har yanzu ba a sallame su ba saboda sun ki baiwa hukumar ta EFCC hadin kai a binciken da ake yi musu, duk da cewa wasun su sun dawo motocin alfarma da sauran wasu kadarorin dake wurinsu.
Title :
Wani Tsohon Shugaban Hafsan Soja Ya Maido Da Naira Milyan 66
Description : Daya daga cikin manyan hafsan sojojin Sama da ake zargi da karbar wasu kaso daga cikin dala milyab 2.1 na kudin sayen makamai wanda ke tsare...
Rating :
5