*Sun Kuma Kama Wani Mai Yi Wa 'Yan Ta'addan Safarar Kifi
A ci gaba da yakar 'yan Boko Haram da dakarun sojojin Nijeriya ke yi, sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan a wasu yankuna daban-daban na jihar Borno. Yankunan sun hada da Kekeno, Gawala, Kukawa da sauransu.
A yayin artabun sojojin sun kashe 'yan ta'addan da dama, inda kuma wasun su suka tsira da raunin harbin bindiga. An kuma kwato babura 13 da kuma jarkoki 39 cike da man injin mota.
A gefe daya kuma, bataliya ta 157 na rundunar sojojin, ta kama wani da ake zargin dan Boko Haram ne, mai suna Mallam Goni a wani gari da ake kira Garin Giwa. Mutumin mai shekaru 55, ya bayyana cewa shi yake yi wa 'yan Boko Haram din safarar kifi.
Yanzu haka ana kan gudanar da bincike akan sa don samun karin haske daga wurinsa.
Title :
Sojojin Nijeriya Sun Sake Yin Nasara Akan 'Yan Bojo Haram A Jihar Borno
Description : *Sun Kuma Kama Wani Mai Yi Wa ' Yan Ta'addan Safarar Kifi A ci gaba da yakar 'yan Boko Haram da dakarun sojojin Nijeriya ke y...
Rating :
5