Daga Adamu Aliyu Ngulde, A Maiduguri
A ranar Asabar din da ta gabata ne rundunar sojin Nijeriya ta sanar cewa, ta sake bude dukkanin manyan hanyoyi da suka yi cudanya da birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno da sauran sassan jihar, bayan da aka shafe
kimanin shekaru uku a rufe saboda hare-haren masu tada kayar baya.
Shugaban rundunar sojin Nijeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai, ne ya
sanar da wannan kaddamarwar da kuma bada umarnin amfani da babura ga sojojin Nijeriya a hedkwatar Dambo'a, dake karamar hukumar Dambo'a a jihar Borno.
Buratai, ya ce sojojin za su yi aiki tukuru domin kullawa da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma.
Buratai ya kara da cewa "Daga yau
hanyar data hade daga birnin Maiduguri zuwa garin Dambo'a, da kuma
Dambo'a zuwa Biu a bude take.
"Za a danka alhakin kulawa da hanyar a hannun Birigediya kwamanda na
25,"
Buratai ya kara da cewa: "Ba na so in ji wani hali na kai hari a kan fararen hula da laifi ko masu motoci a kan wannan hanyar nan gaba".
"Sojojin za su kasance a ankare sa'o'i 24 don tabbatar da cewa hanyoyin a bude suke.''
Ya ce, sun kuma sake bude wasu hanyoyin na daban, ciki har da Maiduguri zuwa Bama, da Maiduguri zuwa Mafa hadi da hanyoyin Dikwa zuwa Gamboru/Ngala da dai sauransu.
"Na san cewa gwamnatin jihar Borno da kuma gwamnatin tarayya sunayin kokarinsu a kan wannan batun,"
Ya bayyana cewa, mun kaddamar da Baburar ne domin samar da tsaro da
kuma dakile kai hare-hare a kan wadanda ba suji ba su ji ba. Har ila
yau ya kara da cewa "An samar da Baburar bataliyar sojojin Najeriya,
muna ganin ta wannan fuskarce za a kara azama domin yaki da 'yan
ta'adda masu tada kayar baya.
"Mun kudiri aniyar yin amfani da Babura yadda ya kamata don tabbatar da cewa hanyoyin sun kasance kamar yadda suke a shekarun baya da kuma kawo karshen 'yan ta'adda da ake
farautarsu a ko'ina suka je," in ji Buratai.
"Zabin al'ummar Dambo'a ita ce zaman lafiya da kuma samun sa'idar
rayuwa.
Buratai ya kara da cewa "Anan sintiri zai taka muhimmiyar rawa don gano wadannan 'yan ta'adda.
"Za mu aika da fastocinsu a sassan
fadin kasarnan don tabbatar da cewa wadanda suka gudu sun shiga hannu.
"Mun yi kira ga jama'a su dubi fostocin a hankali, don gano da kuma bayar da rahoton duk wani mutum da za su iya ganewa kuma su bayar da rahoton asalin inda yake.
"Muna so mu yaba da goyon bayan da jama'a suke badawa, lalle dukkanin 'yan Najeriya sun bada hadin kai, domin
mun samu gagarumin goyon baya a hotuna 100 na farko da yawa daga
cikinsu an gano da kuma cafkesu.
"Ko da yake har yanzu muna neman wasu daga cikinsu muna kira a kan dukkanin 'yan Nijeriya, da su ba mu hadin kai don tallafa wa mu gano wadannan' yan ta'adda a kan wadannan fastoci
Title :
Sojoji Sun Bude Manyan Hanyoyin Jihar Borno Bayan Shekaru Uku A Kulle
Description : Daga Adamu Aliyu Ngulde, A Maiduguri A ranar Asabar din da ta gabata ne rundunar sojin Nijeriya ta sanar cewa, ta sake bude dukkanin manyan...
Rating :
5