Daga Umar Bandi Kofar Kware
Jama’a da dama suna jiran suji ko su ga yadda za ta kaya a tsakanin hukumar EFCC da tsofafin gwamnonin Nijeriya, musamman sanin yadda suka gudanar da mulki a jihohin su, domin a matso kudaden al’umma a hannayen su, tsofafin gwamnonin dasu aka sanya Najeriya a cikin halin da ta sami kanta, domin sunga ruwa ya kai ga wuyansu, daga baya suka yanke hukumcin suyiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da jam’iyyar ta PDP ta waye, domin su tsira da abin da suka kwashe a jihohin nasu, tare da tsoron irin matakan da suke tsammanin Jonathan zai iya dauka akansu.
Da Allah ya kai shi ga samun nasarar, sake darewa akan mulkin kasar, jama’a da dama sun kagara suji an soma lalubo tsofafin Ministoci da tsofafin gwamnoni domin su amayo kudaden al’umma, tare da kwace gidaje da hilaye da suka mayar mallakarsu, da wuraren kasuwanci da suka gigina a ciki da wajen kasar, tare da hannayen jari da suke da su a bankuna da Kamfanoni a ciki da wajen kasar, wasu su daga ciki sun sami nasarar, zama Sanatoci a matakin tarayya, duk yana daya daga cikin matakan da suka ganin zai hana binciken hukumar EFCC ta dora hannayenta akansu, abin da hukumar ICPC tawa tsohon gwamnan jihar Zamfara.
Bai zama wani muhimmin abin da za’a yayata da sunan an kama barawo, idan aka dubi sauran gwamnonin da sukayi zamani da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ko wannenmu yana da tabbacin a lokacin anyi facama da dukiyar jama’a, baya ga kason da ake baiwa jihohin, da kudaden rarar mai, da makuddan kudaden da aka bayar da zimma tallafawa matasa wanda suke kira da suna Shafi, wadanda mafi yawa gwamnonin da yaransu suke rabe kudaden, daga baya suka sake tunani abin yayi yawa, suka rinka rabawa yara talatin ko hamsin dubu goma-goma.
A cewar masu hasashen siyasar kasar, musamman akan abubuwan da suka faru a zamanin mulkin jam’iyyar a matakin kasa da mafi yawan jihohin kasar,akwai shiraruwa masu damar gaske, da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta fitar, da zimmar su zama tsanin zuwa sayawa jam’iyyar PDP, kwarjini da kimar da zata kai ta ga samun nasarar lashe zaben shugaban kasa, wanda ta saki makuddan kudade, amma tsofafin gwamnonin sukayi rubda ciki dasu, domin suna ganin bayar da kudaden, zai iya kawo musu cikas, ga rage yawan magaya bayan su, suka wawushe kudaden suka watsawa wasu daga cikin ‘yan korensu da ke cikin jam’iyyar da suke musu aiki.
Bani tsammani musamman a yankin jihohin Arewar nan musamman a jihohin da gwamnonin suka kammala wa’adin mulkinsu suka dauko wani suka dora, da zimmar ya zama mai rufe barnar da suka tauka a cikin baitalmalin gwamnatin jihar da kananan hukumominsu, a ce za a sami lakawan dake iya ganin tsofafin gwamnonin a matsayin wasu salihai a zamansu masu gaskiya da rikon amana, wadanda ake jin ba wata hujjar kamawa dake iya kaisu ga gurfana a gaban hukumar EFCC.
Wanda yana da wuyar gaske, a wancen zamanin, ace da wani mai matsayi irin na gwamna, ko minista a ce yana iya tsallake siradi, a wajen binciken kudaden jama’a, da aka bashi a mana, amma kilan masu karatu suna wasu gwamnoni ko wani gwamnan day a zama tilo a cikin gwamnonin da sukayi mulki a zamanin gwamnatin Obasanjo da Jonathan basu arzuta kansu da dukiyar al’umma ba.
Title :
Shin EFCC Ta Manta Da Tsofafin Gwamnoni Ne?
Description : Daga Umar Bandi Kofar Kware Jama’a da dama suna jiran suji ko su ga yadda za ta kaya a tsakanin hukumar EFCC da tsofafin gwamnonin Nijeriya...
Rating :
5