Alamu sun bayyana cewa shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Yakubu Dogara da sauran wasu daga cikin jigogin jam'iyyar PDP suna shirin kafa wata sabuwar jam'iyyar kafin zaben 2019, kamar yadda majiyarmu ta National Mirrow ta rawaito.
Wata majiya dake da alaka da ganawar sirrin da aka yi domin kafa sabuwar jam'iyyar, ta bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda aka yi maja da su da wasu membobin jam'iyyar adawa ta PDP, suna daf da hade kansu domin kafa wata jam'iyyar kafin zaben 2019.
Majiyar ta kara da cewa Saraki da sauran wasu 'yan majalisu da suka hada da na majalisar dattijai da na tarayya da wani gwamna daga yankin Arewa maso yamma, wadanda suka yi hannun riga da shugaba Muhammadu Buhari da jigon jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, musamman a lokacin nada mukaman majalisa, da alamu ba za su fito takara karo na biyu a jam'iyyar APC ba, saboda bambancin ra'ayi.
Haka kuma ana zaton cewa rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa bayan nada Ali Modu Sheriff a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP da zargin rashawa da ya yi yawa a jam'iyyar, wanda hakan ya harzuka wasu membobin jam'iyyar, shi ma zai taimaka wajen kafa sabuwar jam'iyyar.
Idan ba a mance ba, wasu daga cikin jigagan jam'iyyar adawa ta PDP suna kauracewa jam'iyyar ba tare da sun koma jam'iyyar APC ba, wanda ake ganin hakan ma wata alama ce na yunkurin kafa wata sabuwar jam'iyyar.
Title :
Saraki, Dogara Da Sauransu Na Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya
Description : Alamu sun bayyana cewa shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Yakubu D...
Rating :
5