Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta sanar da Gianni Infantino a matsayin shugaban hukumar, inda ya maye gurbin Sepp Blatter.
Infantino ya yi nasarar dare kujerar shugabancin FIFA ne bayan ya kayar da shugaban hukumar kwallon kafa na yankin Asia, Sheik Salman da Jerome Champagne da Yarim Ali Bin Al Hussein na kasar Jodan.
Sakamakon zagaye na biyu da aka shiga a zaben, inda ake bukatar kuri'u 104, amma Infantino ya samu kuri'u 115, inda shi zai jagoranci hukumar har zuwa shekarar 2019.
Dan shekaru 45, Gianni Infantino, shi ma dan kasar Switzerland ne, amma yana rike da katin shaidar dan kasa na Italiya. Sannan kuma kafin samun wannan matsayi, shi yake rike da mukamin baban sakataren hukumar kwallon kafa na yankin kasashen Turai.
Title :
Sabon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya, Gianni Infantino
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta sanar da Gianni Infantino a matsayin shugaban hukumar, inda ya maye gurbin Sepp Blatter. Infantin...
Rating :
5