Wata majiya daga Janhuriyyar Nijar, ta rawaito cewa fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya sha ruwan duwatsu agarin
Damagaram.
Babban mawakin siyasar, majiyar ta ceya fuskanci fushin matasa ne a babban filin kwallon kafar Damagaram, inda da kyar aka kubutar da shi ta hanyar yi masa garkuwa.
Matasan Nijar dai sunjima da wannan kuduri, tun bayanwata waka da ya yi da yawunsu wai, acewarsa, a Nijar tazarce ake so. Abinda ya jawo zagi da aibata mawakin atsakanin al'ummar kasar.
Wannan jifar ya tsorata shi har ya fasayin wasan da ya yi niyyar yi a gidanmatasa da raya al'adun kasa (MJC).
A nashi bangaren, shugaba Issoufou
shi ma an fasa masa madubin mota.
Garin da Damagaram da Maradi dai, sun zamawani gandu, inda kowane dan siyasa yake son mallaka saboda tasirinsu asiyasar kasar. Sai dai a dukkan garuruwan shugaban yana fuskantar tsana mafitsauri. Ko a wajen taron, alamu sun nuna daga kauyuka ake kwaso mutanedomin cike kujeru don tsoron tozarci aidon 'yan adawa.
Title :
Rarara Ya Sha Ruwan Duwatsu A Jamhuriyyar Nijar?
Description : Wata majiya daga Janhuriyyar Nijar, ta rawaito cewa fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya sha ruwan duwatsu aga...
Rating :
5