Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya bada labari cewa:
"Akwai mutanen wani gida daga cikin Ansar (mutanen madeenah) suna da wani Rakumi wanda suke 'daukar ruwa dashi.
Watarana sai Rakumin nan yayi musu bore, ya hana su dora masa komai. Sai wasu daga mutanen Madinah din suka garzayo wajen Shugaban Halitta (saww) suka gaya masa halin da suke ciki, kuma suka xe masa rakumin ya Qi daukar ruwan, kuma yanzu haka ga shukokinsu sun fara bushewa, Bishiyoyin dabinonsu duk yayi yaushi saboda rashin ruwa.
Sai Ma'aiki (saww) yace ma Sahabbansa "KU TASHI MUJE". Sai suka tafi zuwa ga wani shinge (waro gona wacce aka katangeta) suka iske rakumin ya rakabe aciki, yaja daaga.
Yayin da mutanen suka ga Manzon Allah (saww) ya nufi wajen inda rakumin yake, sai suka ce "Ya Rasulallahi Rakumin nan fa ya zamanto kamar Mahaukacin Kare, don haka muna tsorace maka sharrinsa".
Sai Annabi (saww) yace "Ai babu abinda zai yi mun".
Mai ruwayar (wato Anas bin Malik) yace : "Yayin da Rakumin nan ya kalli Manzon Allah (saww) - (Kyawun nan da kwarjinin nan suka ratsashi) Sai ya taho kawai gabansa..
Yazo gabansa ya fadi yayi Sujada.
Sai Manzon Allah (saww) ya kamashi ya rike gashin goshinsa, sannan ya shigar dashi cikin wajen aikin.
Sai Sahabbansa suka ce "Ya Rasulallahi, wannan fa dabba ne marar hankali ma gashi yana yin Sujadah agareka. Amma mu da muke da hankali, muka fi chanchanta muyi maka, Sujadah kenan!!".
Da Shugaba (saww) yaji haka sai yace "A'A BAI HALATTA GA WANI MUTUM YAYI MA WANI MUTUM DIN SUJADAH BA.
DA ACE YA HALATTA WANI MUTUM YAYI MA WANI MUTUMIN SUJADAH, DA SAI NA UMURCI MACE TAYI MAIJINTA SUJADAH SABODA GIRMAN HAKKINSA AKANTA.
NA RANTSE DA SARKIN DA NUMFASHINA KE HANNUNSA, DA ACHE TUN DAGA DUNDUNIYARSA (SHI MIJIN) HAR ZUWA TSAKIYAR KANSA DUK GYAMBO NE (WATO RUBABBEN CIWO) MAI 'DIWA DA KUMA RUWA MAI 'DOYI YANA FITOWA TA CIKINSA, SANNAN TA SUMBANCESHI TANA LASHEWA (CIWUKAN DA HARSHENTA) DUK DA HAKAN BATA SAUKE HAKKINSA DAKE KANTA BA".
Hadisi ne Sahihi aduba :
# MUSNADU AHMAD juzu'i na 3 shafi na 159.
# ALBIDAYAH WAN NIHAYAH Juzu'i na 6 shafi na 149.
ABIN LURA

Wannan Mu'ujizar tana karantar damu abubuwa da dama. Daga ciki akwai :
- Girman lamarin Manzon Allah (saww).
- Yadda dabbobi suke girmamashi. Sunyi imani dashi kuma sun san shi Manzon Allah ne (saww).
- Tawadhu'u irin na Manzon Allah (saww). Tunda yana zaune tare da Sahabbansa amma ya tashi ya bar abinda yakeyi. Don magance damuwar wani.
- Rashin halaccin yin Sujadah ga wanin Allah.
- Girman hakkin da Miji yake dashi akan matarsa.
Anan nake Qara jan hankalin 'Yan uwa mata, Musamman masu ganin cewa Mijinsu bai isa suyi masa kaza da kaza ba, cewa Suji tsoron Allah su lura da sakon da wannan hadisin yake kunshe dashi.
An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP -(1) aranar Talata 16-02-2016.

Please like Us On  Facebook

Follow us on Twitter

Title :
Rakumi Yayi Sujadah Agaban Sa
Description : Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya bada labari cewa: "Akwai mutanen wani gida daga cikin Ansar (mutanen madeenah) suna da wani Rakumi ...
Rating :
5