A yau (Juma'a) ne ake daura auren fitaccen jarumin finafinan Hausan nan kuma da darakta, wato Ishaq Sidi Ishaq, wanda aka fi sani da Dan Kwalisa, bayan tsawon lokacin da 'yan uwa da aka abokan sana'arsa har ma da masoyansa suka dauka suna dokin ganin ranar aurar nasa.
Ishaq, wanda qwararre ne wajen bayar da umarni a finafinan hausa, zai auri sahibarsa ne mai suna Naseeba Usman Wada, inda za a daura auren a garin Minna babban birnin jihar Neja.
Bayan bulluwar hotunan jarumin da amaryar ta sa a yanar gizo, jama'a da dama sun ta taya shi murna tare da san barka, musamman abokan sana'arsa da kuma masoyansa wadanda suka jima suna dokin ganin ranar auren nasa.
Ishaq, wanda kusan wannan shine auren sa na farko, kamar yadda bincike ya nuna, a baya ya yi soyayya da jaruman fim irin su Halima Adamu Yahaya, Aina'u Ade, Umme Ibrahim (Zee-zee) da sauransu, amma Allah bai sa aure ya shiga tsakaninsa da daya daga cikin su ba.
Source Rariya
Title :
Photos: Yau Aka Daura Auren Ishaq Sidi Ishaq
Description : A yau (Juma'a) ne ake daura auren fitaccen jarumin finafinan Hausan nan kuma da darakta, wato Ishaq Sidi Ishaq, wanda aka fi sani da Da...
Rating :
5