Iyaye Da 'Yan Uwan Wani Yaro Dan Shekara Biyu Sun Guje Shi Saboda Zarginsa Da Maita
Wani dan shekara biyu da haihuwa ya tsinici kansa cikin kuncin rayuwa sakamakon kaurace masa da iyayensa da 'yan uwansa suka yi sakamakon zarginsa da maita da suke yi.
Wata Baturiya da ta taimaka masa wajen kula da lafiyarsa, bayan ta tsince shi a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom, ta tabbatar da cewa sakamakon kauracewa yaron da 'yan uwansa suka yi ne ya sa shi yake ta garari akan titi har na tsawon watanni, inda jama'a masu giftawa suke taimaka masa da abinci.
Baturiyar, wadda 'ar kasar Denmark ce mai suna Anja Ringgren Loven, ta kara da cewa yaron wanda take yi masa lakabi da 'Hope' ya jima yana cikin matsanancin hali.
Ta ce a lokacin da ta tsince shi, akwai bukatar a kara masa jini da ba shi magunguna don ganin ya samu lafiya.
Baturiyar ta sanar da labarin halin da yaron yake ciki ne a shafinta na facebook, inda ta bukaci da a taimaka da kudi domin daukar nauyin kula da lafiyarsa, ci da sha da karatunsa.
Baturiyar dai ita ke da gidauniyar tallafawa karatu da ci gaban yara a yankin Afitika, wanda ta kirkira donin ceto yara marasa galihu.
A yayin da ta kara fitar da sanarwa a shafinta na facebook, kan halin da yaron yakw ciki bayan ta dauki nauyin kulawa da shi, a ranar Juma'ar da ta gabata, ta bayyana cewa yanzu haka yaron yana kan murmurewa. Abin da ya rage kawai shine ya soma magana.
Ta ce akwai yiwuwar ya fara magana idan ya soma shiga cikin yara 'yan uwansa da zarar an salleme shi daga asibiti.
Title :
Photos: Yaro Dan Shekara Biyu Wanda Iyayen Sa Suke Zargin Sa Da Maita
Description : Iyaye Da 'Yan Uwan Wani Yaro Dan Shekara Biyu Sun Guje Shi Saboda Zarginsa Da Maita Wani dan shekara biyu da haihuwa ya tsinici kansa...
Rating :
5