Allah shine yakan yi yadda yake so babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi. Wata mata mai suna Sakirat Rasaq ta haifi ya'ya biyar a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan ta jihar Oyo.
Mijin matar wanda mallamin Islama ne a wata makaranta dake garin Ibadan, Alfa Yusuf Razaq ya ce dukanin yaran suna cikin koshin lafiya har da mahaifiyarsu.
A cikin jariran dai akwai maza uku mata biyu. Kuma kafin wannan haihuwa dai matar tana da ya'ya biyu.
Jama'a da dama na ta tururuwa zuwa asibitin koyarwar domin su ga ikon Allah. Da yawa daga cikin mutanen suna bayar da gudumuwarsu walau na kudi ko kuma abinci har ma da sutura.
Title :
Photos: Wata Mata Ta Haifi 'Ya'ya Biyar A Jihar Oyo
Description : Allah shine yakan yi yadda yake so babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi. Wata mata mai suna Sakirat Rasaq ta haifi ya'ya biyar a asibit...
Rating :
5