Wannan baiwar Allah mai suna Habiba Shaba Ibrahim ta bace tun shekaranjiya.
Bayan da motar ta samu matsala a unguwar Kubuwa dake Abuja, sai ta shiga motar tasi domin ya kai ta gida, amma gidan da ba ta iso har zuwa yanzu kenan ba.
Ta bar yara uku a gida, kuma tana dauke da cikin wata biyar. Don haka 'yan uwanta suke barar addu'o'inku domin Allah ya bayyana ta duk inda take. Tare kuma da ba ku cigiyarta.
'Yan uwa da abokan Habiba sun bayyana ta a matsayin kamilalliya kuma wacce ta iya zama da jama'a.
Title :
Photos: Ana Cikiyar Wanna Baiwar Allah
Description : Wannan baiwar Allah mai suna Habiba Shaba Ibrahim ta bace tun shekaranjiya. Bayan da motar ta samu matsala a unguwar Kubuwa dake Abuja, sai...
Rating :
5