Wannan shine hoton da wani bawan Allah ya yi posting akan dukan da malamin islamiyya ya yi wa yaronsa!
Wannan ya nuna abubuwa kamar haka:
1. Rashin kwarewa akan aiki da ke damun da yawa cikin malaman islamiyya
2. Rashin tausayi a zuciyar wasu wadanda su ya kamata su zama abin koyi wajen rahama, musamman ga kanana da masu rauni
3. Jahilci ko karamin sani kan koyarwar sunna wajen laduban ladabtarwa da gyaran kuskuren yara. Misali, Manzon Allah (saw) yayi koyarwa na shekara 23, wannan shi ne mialin tsarin karantarwarsa?
4. Karancin sa ido daga shugabannin gudanarwa na makarantunmu akan aiyukan malaman da ke karkashinsu. Ina da yaqinin Allah zai yi bincike akan irin wadannan munanan misalai, kuma tabbas, duk wanda ke da hannu akan irin wannan za a nemo shi!
5. Yawaitar irin wadannan matsaloli a makarantun addini. Wannan kawai misali ne na wanda aka nuna mana. Ina wadanda ba su da gatan wanda zai bayyana nasu wa duniya? Ina wadanda iyayensu zasu goyi bayan malamin akan wannan kuskure bisa tsammani hakan shi ke kawo albarkar karatu? Ina wadanda za a yi musu rotse ko mummunan rauni har a kwanta jinya, duk da sunan koyarda addini...?
NASIHA GA MALAMAI
1. Mu sani cewa yayan mutane amana ne a hannunmu kuma Allah zai tambaye akan wannan amana.
2. Wajibi ne mu zama jagorori wajen nuna kyawawan dabi'un Manzon Allah wajen karantarwa, musamman hakuri, juriya, yafiya da rahama.
3. Ladabtarwa tana da matakai da kuma hanyoyi daban daban. Ba koyaushe ake duka ba. Ba kowa ake duka ba. Ba kowane laifi ake wa duka ba. Ba ko ina a jiki ake duka ba.
4. Tarbiyyar musulunci ita ce malami ya nuna wa dalibansa yadda zasu yi ladabi ta hanyar kauna ba ta hanyar tsoro ba.
5. Akwai bukatar samar da kyakkyawan tsari a makarantunmu na alaka tsakanin iyaye da malamai da shugabannin makarantu don magance aukuwar irin wadannan matsaloli tare da hadin kai wajen ladabtar da malamin da ya karya doka.
6. Akwai bukatar makarantu su rika shirya workshops akan tsarin karantarwa da ladabtarwa a Musulunci don gudun aukuwar irin wannan, tare da samar da tsauraran dokoki akan wanda ya saba tsarin da aka gindaya bayan an karantar da malamai wadannan tsare-tsare. Ina tuna na gabatar da kasida akan tsarin karantarwa da ladabtarwa a makaratun al-Qurani kwanakin baya wa malamai. Ina gani sauraron irin wadannan darussa zasu taimaka wa malamai da hukumomin makarantu.
A karshe ina mika jaje ga wannan yaro da iyayensa akan wannan abin tausayi.
Allah Ya albarkaci wannan yaro da albarkar al-Qurani tare da sauran yayanmu gaba daya.
Title :
Nasiha Ga Malamai - Mansur Isa Yelwa
Description : Wannan shine hoton da wani bawan Allah ya yi posting akan dukan da malamin islamiyya ya yi wa yaronsa! Wannan ya nuna abubuwa kamar haka: ...
Rating :
5