DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Da safiyar wannan rana ta Laraba ce, wani matashi dan kimanin shekaru 25 ya rasa ranss, biyo bayan banke shi da wata mota ta yi, a lokacin da yake kokarin daukar naira Ishirin dinsa da ta fadi akan hanya, a titin Byepass dake Kaduna.
Shaidun gani da ido sun bayyanawa RARIYA cewar, mutumin yana tafiya ne lokacin da iska ta dauke masa naira 20 din a cikin aljihunsa, sannan iskar ta kada ta kan titi, shi kuma cikin gaggawa ya bi naira 20 din ba tare da ya duba titi ba, a dai-dai wannan lokacin ne wani mai mota da ya fito a guje ya bi ta kansa.
RARIYA ta samu lekawa Asibitin Fada dake Kakuri inda aka kai shi, kuma mutumin ya rasa ranshi bada jimawa ba, saidai hukumomin Asibitin sun hana manema labarai daukar hoton gawar, kamar yadda suka bayyana cewa doka ne a tsarin Asibitin.
Title :
Naira 20 Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Wani Mutum A Jihar Kaduna
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Da safiyar wannan rana ta Laraba ce, wani matashi dan kimanin shekaru 25 ya rasa ranss, biyo bayan banke shi d...
Rating :
5