Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayan sa na ganin an kafa kasar Falasdinu don ganin an kawo karshen matsalolin da Falasdinawa ke fuskanta a Gabas ta Tsakiya.
.
Yayin da yake ganawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani, shugaba Buhari ya ce Nijeriya na goyan bayan daukacin kudirorin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su wajen samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
.
Buhari ya shaidawa Sarkin cewar Nijeriya za ta hada kai da Qatar har sai ta ga Falasdinu ta samu biyan bukata.
.
Idan dai ba’a manta ba a shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ki kada kuri’ar goyan bayan Falasdinu a kwamitin Sulhu a karkashin shugabancin Goodluck Jonathan
Title :
Na Goyi Bayan A Samar Da Kasar Falasdinu
.
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayan sa na ganin an kafa kasar Falasdinu don ganin an kawo karshen matsalolin da Falasdina...
Rating :
5