Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce duk masu zagin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari munafukai ne masu son kashe kasar ta hanyar cin hanci da rashawa.
A yayin da yake bayani a kasar Uganda bayan ya kammala sanya idanu a zaben shugaban kasar da aka gudanar, Obasanjo ya bayyana cewa, hakikanin gaskiya munafukai da barayin gwamnatin ne kadai ke zagin gwamnatin Buhari, domin ya san cewa talakawan kasar baki daya suna bayan shugaba Buhari.
Obasanjo ya bayyana zaben da aka gudanar a kasar ta Uganda a matsayin zabe mai cike da magudi.
Daga karshe Obasanjo ya ce yana tare da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dari-bisa-dari, kuma ya zama dole ya taimakawa gwamnatin Buhari domin ya cika alkawarin da ya yi wa 'yan Nijeriya.
Title :
Munafukai Da Barayin Gwamnati Ne Ke Sukar Gwamnatin Buhari - Obasanjo
Description : Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce duk masu zagin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari munafukai ne masu son kashe kasar ta han...
Rating :
5