Lionel Messi ya ba wani yaro kyautar rigarsa bayan da ya ga hotunan yaron a shafukan intanet sanye da rigar ta leda da aka yi da leda.
Yaron mai suna Murtaza Ahmadi dan shekara 5, daga Afghanistan, dan gani-kashe-nin fittacen dan kwallon ne, wanda soyyayarsa ta sa ya yi rigar Messin da leda, a ka kuma sa shafukan intanet.
Hotunan Murtaza sun yi farin jini, a sakamakon hakan ya sa Messin ya aika wa da yaron rigarsa ta hakika, da kuma sa hannunsa a jiki.
Messi wanda ya taba lashe kambin zakaran kwallon kafa ta duniya har sau biyar, shi ne jakadan Asusun Kanannan Yara na Majalisar Dinkin Duniya
Title :
Messi Ya Baiwa Yaro Rigarsa
Description : Lionel Messi ya ba wani yaro kyautar rigarsa bayan da ya ga hotunan yaron a shafukan intanet sanye da rigar ta leda da aka yi da leda. Yar...
Rating :
5