Hakika iyaye suna da babban matsayi a musulunci domin Allah madaukakin sarki ya yi gargadi da kuma wasiya ga ‘ya’ya maza da mata akan su kyautatawa iyayensu, tare da yi musu duk abin da suke bukata matukar bai sabawa fadar Allah da kuma fadan manzo { S.A.W } Ba. Allah mai girma da daukaka ya yi gargadi da kuma kwadaitarwa a cikin wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma kuma ya yi bayanin rahama da baiwa tare da samun yardarsa ga duk wanda ya bi iyayensa kuma, ya yi tanadin azaba ga ukuba ga wanda duk ya fandare kuma ya kuntatawa iyayensa, tare da yi masa mumunan sakamako a ranar tonan asiri wato rana alkiyama.
Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin alkur’ani ma girma:- mun yi wasiya ga dan adam game da mahaifansa biyu da kyautata musu, Mahaifiya ta dauki cikin ka/ki a wahale kuma ta haife ka/ki a wahale, cikinka da yayenka wata talatin ne duk cikin wahala, To a cikin wannan aya Allah madaukakin sarki yayi mana wasiya wato mu ‘ya’ya akan mu kyautatawa iyayenmu musamman mahaifiya wato uwa, wacce saboda irin tsanance-tsanance da ta shiga tun farkon samun ciki har zuwa ranar haihuwa
wanda yake ita ce rana mafi shiga tsanani a gareta domin lokacin da mace ta gurfana zata haihu, inda zaka dauko allura ka soki idonta da ita to bazataji komai ba. To YAN UWA BAYIN ALLAH YA KAMATA MU HALKANTA MUSAN MATSAYIN IYAYE MUYI MUSU BIYAYYA, ALLAH YA BAMU IKON BIYAYYA A GARESU. Ameen summah Ameen
Title :
MATSAYIN MAHAIFIYA A MUSULUNCI
Description : Hakika iyaye suna da babban matsayi a musulunci domin Allah madaukakin sarki ya yi gargadi da kuma wasiya ga ‘ya’ya maza da mata akan su kya...
Rating :
5