A ci gaba da wasanin cin kofin Firimiya na kasar Ingla a yau Lahadi, an yi karan batta tsakanin wasu manyan kungiyoyin kwallan kafa guda biyu a kasar.
Manchester united Wanda ake wa lakabi da The red Devils ta lallasa Arsenal (The gunners) da ci 3-2 a filin wasa na Old Trafford.
Marcus Rashford mai shekaru 18 ne ya ci wa Man U kwallaye biyu, yayin da Ander Hereira ya ci ta uku. A yayin da tsohon dan wasan Manchester United wanda ya koma Arsenal, Danny Welbeck da Mesut Ozil suka ci wa Arsenal kwallaye biyu.
Wannan kaye da Arsenal ta sha babu shakka zai kasance koma baya ne a kokarin ta na lashe kofin a kakar wasanin ta bana.
A daya wasan kuwa Tottenham ta doke Swansea ne da ci 2-1
Saukar Da Video wasan
New Video : Manchester United 3 Arsenal 2