DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Kwamitin bincike kan tarzomar da ta faru a tsakanin Sojoji da 'Yan Shi'a watannin baya a Zaria, wanda gwamnatin El Rufa'i ta kafa, zai fara zaman sauraren shaidu da korafe-korafen jama'a gobe Litinin, a gidan gwamnati na Hassan Katsina dake Kaduna.
Kwamitin ya kara tsawon wa'adin sauraren koken jama'a, wanda a baya aka ayyana ranar 14 ga watan Fabarairu, ya zuwa ranar 22 ga watan, domin baiwa jama'a daman gabatar da korafe-korafen su.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa, wacce ta samu sanya hannun Sakataren Kwamitin mai suna Dakta Bala Babaji, inda ya ce tuni Shugaban Kwamitin binciken Mai Shari'a Muhammad Lawal Garba, ya karbi koke sama da 100 daga bangarorin daban-daban na addinai, 'yan kasuwa, da sauran jama'ar gari.
Sanarwar ta bayyana cewar sauran jama'a mazauna Zaria da kewaye, wadanda ba za su iya isowa inda Kwamitin yake zama a Kaduna ba, za su iya mika takardun kokensu a Sakatariyar Karamar hukumar Zaria.
Kwamitin binciken zai binciki musabbabin faruwar rikicin, sakacin da aka yi a baya, da kuma hanyar magance rikicin a nan gaba.
Shugaban Kwamitin binciken ya kuma bukaci dukkanin wadanda guguwar rikicin ta shafa, kama daga kan Sojoji da 'yan Shi'ah da sauran jama'ar gari, da su baiwa kwamitin goyan bayan da ya dace domin kai wa ga nasara.
Ana sa ran Kwamitin mai Wakilai 13, zai lashe makonni shida yana zama, sannan ya mika rahotonsa ga gwamna Nasiru El- Rufa'i bayan kammala wa'adin zaman na farko.
Title :
Kwamitin Bincike Kan Rikicin 'Yan Shi'a Da Soji, Zai Fara Zama
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Kwamitin bincike kan tarzomar da ta faru a tsakanin Sojoji da 'Yan Shi'a watannin baya a Zaria, wanda ...
Rating :
5