Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da kara da Shugaban Majalisar Dattijai, Senata Bukola Saraki ya shigar gabanta, kan tuhumarsa da ake na kin bayyana kadarorinsa a lokacin da yake gwamnan Kwara.
Kotun ta bukaci Saraki da ya koma Kotun da'ar Ma'aikata domin amsa tuhumar da ake yi masa,
Saraki ya shigar da karar ne a kotun koli domin kalubalantar kotun daukaka kara da ta yi watsi da bukatun shin a yin watsi da shari’ar.
Saraki na fukantar caje-caje 13 kan rashin bayyana gaskiyar kadarorinsa a zamanin da yake gwamnan Kwara a shekarar 2003.
Title :
Kotun koli ta yi watsi da bukatar Saraki
Description : Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da kara da Shugaban Majalisar Dattijai, Senata Bukola Saraki ya shigar gabanta, kan tuhumarsa da ake na ki...
Rating :
5