Annabi (Saww) yace, KU TUNASAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANARDA MUMINI. inamu Buhari ya ruwaito.
Ina tuna tar damu cewa, ako da yaushe kafin bacci ya daukeka ka aikata wadannan abubuwa;
Ka sallaci shafa'i da witri, dan baka tabbacin tashi daga baccin da zakayi.
Kayiwa kanka hisabi! Wato ka auna ayyukanka na alkhairi dana sharri da ka aikata awannan yini, idan na alkhairin sukafi yawa, to sai kayiwa Allah godiya, kuma kayi qoqarin tabbata akan haka ayinin gobe.
Idan kuwa kasami akasin haka (wato na sharrin yafi na alkhairin yawa), to sai kayi qoqarin yawaita aikin lada kafin bacci ya daukeka, kamar karanta "suratul ikhlaas" wato qulhuwallahu, Wadda Annabi (saww) ya fada
cewa tana daidai da kashi daya cikin uku na alqur'ani.
Da yawaita fadar "Sub-hanalla-hi wabi hamdihi subhaanallaahil aziim Wadanda suma Annabi
(saww) yace: suna da nauyi akan mizani a gobe Qiyama.
Ko kuma fadin Walhamdulillaahi saboda itama Annabi (saww) yace: tana cika mizani.
Ko fadin Subhaanallaahi walhamdulillaahi wadannan kuma yace: suna cika abinda ke
tsakanin sama da kasa.
ko kuma kowacce cikin Suhaanallahi da walhamdulillaahi tana
cikawa. da sauran makamantansu.
Kuma kayi qoqarin gyarawa ayinin gobe me zuwa, ya zamto ayyukanka na alkhairin sufi na sharri yawa.
Kada ka manta da zikirai tareda addu'o'i da shari'ar musulunci ta koyar dakai yayin kwanciya bacci.
Yin Alwalla kafin Kwanciya, domin Annabi (saww) yace, Wanda duk yayi Alwalla ya kwanta za'a rika rubuta masa lada har ya tashi daga bacci.
Ka debe Hassadar kowa a zuciyarka, domin idan kana kwana da hassada baka taba ci gaba a harkokin rayuwa, idan kuma baka kwana da hassada zaka rika gamuwa da nasara a dukkanin harkokinka.
Ka sani duk wanda ka turawa wannan kuma ya aikata hakan to duk ladar da aka bashi kaima za'a baka kwatankwacin haka.
YA Allah ka Sa mu dace duniya da Lahira, Allah ka samu a ceton Annabi (saww), Allah kuma ka sa Mu ganshi a Baccin mu da Zahirin mu.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA
Title :
Ko Wannan Sako Yan Isa Gareka
Description : Annabi (Saww) yace, KU TUNASAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANARDA MUMINI. inamu Buhari ya ruwaito.
Ina tuna tar damu cewa, ako da yaushe k...
Rating :
5