Baiji wata fargaba ba kasancewar yasan iyayensa suna da saukin fahimta ko kadan basu da daukar zafi musamman kan abunda yake halal.
Daren litinin ya shiga gidan. Yaci sa'ar samun iyayen nasa zaune a falon Abbansa.
Ya karasa cikin ladabi ya russuna ya gaidasu. Cikin sakin fuska suka amsa mishi da tambayar iyalinsa.
"Duk suna lafiya."
Ya danyi shiru bayan ya gyara zama ya zauna, Mahaifinsa ya dubeshi yana nazari
"Ya dai malam,akwai magana ne?"
Ya shafi sumarsa yana murmushi
"Daman zuwa nayi na sanar maku inason k'ara aure."
Cike da mamaki Alhaji ya dubi Hajja wacce tayi shiru batace uffan ba. Ya maido dubansa ga Jafar
"Aure fa kace malam? Yanzu kai zaka iya rike mata biyu?"
Jafar har lokacin bai dago kanshi ba yana mai jin nauyi bai iya amsa mishi ba. Can kuma Alhaji ya numfasa
"Toh! A ina ita kuma yarinyar take?"
Ya numfasa cikin jin dadi
"Anan Kano take unguwar yakasai."
Alhaji ya jinjina kanshi
"Shikenan,zanyitunani sannan ina mai shawartarka ka dage da adduar neman zab'in Allah,idan lamarin mai tabbatuwa ne mai alheri ne,Allah Ya tabbatar. Komai na lamuran duniya yana bukatar a nemi zabin Ubangiji,mutum zaifi ganin daidai cikinsa. Allah Yayi jagora,kaje zamu ga abunda hali yayi."
Daga haka sukayi sallama,Jafar ya tafi cike da kwarin gwuiwar samun muradin zuciyarsa.
*****
Sati daya da yin hakan,Alhaji tuni sun gama amincewa da dan uwansa (mahaifin siyama) akan batun auren Jafar. A cewarsa ai k'ara raya sunnar ma'aiki ne babu wani laifi."
Da wannan suka kirayi Jafar sukayi mishi nasiha mai ratsa zuciya akan ya kwatanta adalci,sannan ya sanar da matarsa. Abba kuwa yace babu dalilin da saita amince zaiyi aure,jafar ya nemi izni wajen yarinya aje ayi maganar aure kawai amma koda Siyama bata kwantar da hankalinta ba babu abunda za'a fasa!
*****
Haris ya zubawa Jafar ido jin wani zance kamar a mafarki..
Jafar murmushi kawai yakeyi yana shafar sumarsa. Haris ya girgiza kansa
"A baya idan naji kana batun k'ara aure,ban taba kawowa dagaske bane. Koda na kawo da gaske kakeyi zakayi aure ban zaceshi anan kurkusa ba."
Jafar ya daga kafada kadan
"Kasan lamarin Ubangiji,ni kaina banma yi zaton zan kara son wata diya mace ba bayan Siyama,sai gashinan Allah Yayi."
Haris ya jinjina kansa yana mai gyara zamansa a kujerar da yake zaune akai cikin shagonsu Jafar.
"Haka yake,Hadiyyar ce dai?"
Jafar ya lumshe ido kadan yana murmushin jin dadin an kirayi sunan masoyiyarsa
"Itace, nayi maganar turo magabatana gareta,tace na jira mahaifiyarta zata sanarwa yayyun mahaifin nata kasancewar mahaifinta ita ya rasu. Duk lokacin da suka yanke sai aje."
Haris yana dariya,suka tafa
"Dakyau mutumin,kace babu kama hannun yaro. Toh yaushe za'a kaini na ganta?"
Jafar ya harareshi
"Waikai akanme ja matsu daka ganemin matata ne? Wataran ai za'a hadu ko?"
Haris ya juya ga ibrahim
"Jimin wannan zancen ibro,yanzu ni haka nayi mishi? Inace saida na nuna maku hoton Rahma?"
Ibrahim yayi dariya
"Gaskiyane,kumamuka yaba."
Jafar ya tabe baki
"Malam ni ba haka tsarina yake ba kaji ko? Bana son nuna iyalina kafin na auresu."
Haris yana dubansa cike da zargi
"Eh amma duk da haka kasha kaini wajen Siyama kafin aurenku.."
"To naji,akan wannan dai ra'ayina ya chanja. An daina wannan yayin."
Sukayi dariya,Haris ya amsa da
"Toh,idan dai lokaci yazo zamu ji mu gani."
Haka sukayita hira abinsu.
*****
Mama ta samu yayan mahaifin Ladi,Mamman tayi mishi maganar zuwan magabatan Ladi. Yayi farin cikin jin haka,babu bata lokaci yace zai sanarwa sauran yan uwan maza koda a gobe ne sai suzo.
Bayan Ladi ta gama sauraron bayanin Mama,ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin wani sanyin dadi yana ratsa zuciyarta. Mama ta kara da cewa
"Saiki buga ki sanar mishi ko?"
Murmushi tayi ta amsa da toh.
Ta sanarwa Jafar shima cikin zumudi yaje ya samu mahaifin Siyama,kasancewar komai na ragamar auren ya koma hannunsa. Ya sameshi a falonsa yayi mishi batun sun amince a turo gobe. Abba yana murmushi yace
"Kai madallah,shikenan Allah Ya kaimu goben sai muje."
Jafar ya amsa,sannan ya mike ya fita.
Hajiya dake daki ta fito ta zauna gefen Abba tana kallonshi
"Abban Siyama,maganar me naji kuna yi kaida Jafar?"
Ya daure fuska tamau
"Banason ana shigarmin maganar da babu ruwan mutum ciki."
Ta tabe baki
"Yo,laifine don na tambaya?"
Bai kara cewa komai ba,bayason tasan zancen yanzu sanin rashin hankalinta yanzun nan saita yiwa Siyama hudubar shaidan a tadawa Jafar hankali.
Ita kuwa Hajiya wacce taji Abba yana batun zasuje gobe,tunanin inda za'aje takeyi,karshe dai ta watsar da zancen.
*****
Nan ma Jafar ya sanarwa Hajja,tayi shiru kafin tace
"Ka sanarwa Siyama?"
Ya girgiza kai
"Ba yanzu ba hajjah."
"A'a,lallai ka sanar mata banaso ta tsinci maganar a waje abun ya zamto rigima. Ka samu ka sanar mata ta hanyar data dace."
"Toh Hajjah."
*******
"Alhamdulillah,kai naji dadin wannan zancen Kakana. Na manta rabon dana tsinci kaina cikin tsabar farin ciki irin wannan. A ina yarinyar take?"
Anti habiba ke tambayar cikin tsabagen farin ciki
"Anan garin take, Yakasai."
Anti habiba baki yaki rufuwa
"Ai gwara ka k'ara auren nan kakana kaima hankalinka ya kwanta. Ko babu komai za ayi maganin wadannan marasa tsoron Allahn. Yanzu dai kenan muna gama hidimar bikin Bahijja sai naka? Gida daya zaka hadasu?"
Jafar cikin damuwa yace
"Toh,ganinan dai. Inason hadasu amma ina tsoron kada Hadiyya tak'i don yarinya ce gwanar tsafta,bazata so kazanta ba."
"Ka hadasu kakana,zaifi. Kada ka damu,babu abunda zai faru. Yanzu ka sanarwa ita Siyamar?"
"A'a tukunna,nafiso sai an sanya ranar."
Ta jinjina kanta tana murmushi
"Tabbas gwara hakan,Allah Yasa ayi muna raye."
"Amin anti."
******
Wata biyu aka sanya bikin Hadiyya da Jafar..
Har lokacin Jafar ya kasa sanarwa Siyama batun aurensa. Haka kawai yaji yana tsoron bacin ranta. Acikin sati uku ya kammala had'a lefensa tsaf da taimakon kudaden daya samu wajen Abban Siyama da Alhajinsa. Komai ya kammala don Anti Habiba ya damkawa,duk da alokacin bata zama saboda shirye shiryen da suke na auren Bahijja wanda alokacin sauran kwana biyu kacal. Sun tsara ana kammala hidimar bikin Bahijja za a mika lefan Hadiyya.
Suna zaune a falon anti habiba bayan ya kammala ganin lefen yana murmushin jin dadi ya dubeta
"Masha Allah,komai yayi kyau antina."
Tayi dariya
"Ai kam,kaya sunyi kyau. Saidai har yau ka gaza kawomin kanwartawa na gani ko?"
Yana murmushi ya shafi sumar kansa
"Kiyi hakuri antina,zan kawo maki ita kafin ku soma bikin Bahijja."
Ta jinjina kanta
"Ai shikenan toh,Allah Yasa."
"Amin."
****
Hakan kuwa akayi,takanas Jafar ya hayo d'an adaidaita sahu suka dauki Basma da Hadiyya zuwa gidan Anti Habiba. Dayake mai adaidaitan d'an gida ne,har kofar gidan anti habiba ya kaisu. Anan suna iske Jafar zaune yana hira da wani kanin mijin anti habiba,Suleiman. Ganinsu yasa suka mike,Jafar yana kashe Hadiyya da wani irin kallo da su kadai sukasan ma anarsa. Ta dan lumshe masa ido tana murmushi,ai sai ta rud'ashi. Ji yayi kamar ya sumbaci idanuwanta da suka sha ado da eyeshadow tayi fes da ita.
"Sannunku da zuwa."
Maganar Suleiman ce ta katse mishi tunani,ya bar kallon Hadiyya,ya maida dubansa ga Basma yana amsa gaisuwarta. Hadiyya ma ta gaishesu. Suleiman yana dariyar zolaya ya dubi Hadiyya
"Ko ba'a fadamin ba nasan kece amaryarmu don na lura da kallon da ogan ke jifanki dashi."
Jafar da Basma sukayi dariya,shima yana tayasu. Hadiyya murmushi kawai tayi tana mai satar kallon Jafar. Ya daga mata gira
"Ashe zaka iya ganeta. Ku shigo ciki."
Jafar yayi gaba,suna biye dashi. Anti tana zaune bayan ta kammala yiwa amarya bahijja gyaran jiki taji sallamarsu.
Cikin fara a ta amsa,
"Maraba lale da amaryarmu. Bismillah ga wuri ku zauna."
A kunyace suka soma kokarin zama a k'asa,anti tayi saurin dakatar dasu
"Kai haba dai a kasa? Maza ku hau saman kujera."
Dakyar suka zauna,Hadiyyah ji takeyi kamar kasa ta tsage ta shiga.
Anti tana murmushi ta amsa gaisuwar da sukeyi gareta kafin ta hau duban fuskokinsu. Hadiyya dake faman sussune kanta ta zurawa ido
"Na gano amaryar tamu,d'agomin fuskarki na ganki sosai mana."
Jin haka yasa Hadiyya kara jan gyalenta,Jafar ya karasa ya soma kokarin janye mayafin
"Bari ki ganta sosai antina."
Suleiman na dariya yace
"Kaidai baka da kunya wallahi."
Hadiyya ta hau dariya ciki ciki,anti ta maka mishi filon kujera
"Ina fa yaga ta kunya? Ku tashi ku fita ku barni da kanwata."
Jafar yana dariya suka fice da suleiman. Daidai nan Bahijja ta fito daga daki,tayi wanka saboda kurkum da tayi,duk saita chanja ta kara haske da kyau. Ganin wadanda ke zaune ta fadada fara'arta
"Ashe yayar tawa ta iso. Bari a kawo maku ruwa."
Tayi kicin da sauri,anti ta dubi basma tana murmushi
"Menene sunanki ke?"
"Basma."
Ta gyada kanta ta maida dubanta ga Hadiyya
"Kinga Hadiyya ki saki jikinki,ki daukeni tamkar yayarki. Menene na wannan noke noken iye? Don Allah ki saki jikinki damu muna kaunarki."
Hadiyya ta gyada kanta,har Bahijja ta dawo dauke da ruwa da lemo sai cin cin da meatpie. Ta ajiye musu
"Toh amaryar yayana,bismillah."
Ta soma zuba lemun ta mika mata,anti habiba ta mike jin tsayuwar mota
"Inajin yaran nan ne suka dawo daga makaranta bari na gani."
Ta fita,Bahijjah data mikawa Basma ta dubi Hadiyya
"Saiki bude fuskar don Allah kinga dai ni kanwarki ce babu kunya tsakaninmu ko ya kikace Basma?"
Basma ta gyada kanta tana dariya
"Hakane yar uwa,mene sunanki?"
Bahijja tayi murmushi
"Bahijja,aurenajibin nan za'a soma."
Sai lokacin Hadiyya ta bude fuskarta ta dubi Bahijja tana murmushi a kunyace
"Allah Sarki,ashe kece Bahijja?"
Bahijja take karewa fuskar hadiyya kallo tana mai yaba kyawunta mai sanyi ta fadada fara'arta
"Nice anti deeya. Masha Allah,ashe don kinsan kina da kyau shiyasa kika k'i nuna mana fuskar taki ko?"
Sukayi dariya,
"Ba haka bane nauyin anti nakeji wallahi."
"Toh karki damu,indai anti ce wallahi babu ruwanta. Sau da yawa itace abokiyar shawarata ma."
Haka Hadiyya suka sake sunata hira da Bahijja kamar sun san juna. Dawowar anti ya sanyasu Hadiyya yin shiru.
Ta dubi fuskar Hadiyya dake a bude
"Inye,ashe haka amaryar tamu take da kyau. Lallai dole ki dunga boye fuskarki."
Murmushi kawai Hadiyya tayi.
Sun jima wajen anti sannan suka fito bayan anti ta cikasu da kyautuka.
A zauren gidan jafar ya tsare Hadiyya da hira. Kamar kada su rabu yakeji dakyar ta lallabashi sukayi sallama,wanda ya kawosu ne ya maidasu. Nan ma kafin a ja adaidaitan ya jima tsaye,karshe ma yace mata zai shigo anjima.
******
Duk wannan budurin da akeyi,Hajiya Siyama bata da labarinsa har sai ranar yinin Bahijja........
Ko ya akai ta sani..?