Ya gama sace zuciyarta,a yau saita kara ganin ya kara kyau agareta. Da wannan farin cikin ta fada shagonsu.
******
Karfe takwas na dare sai gashi yayi kiranta. Lokacin tana cin abinci,har ya gama ringing bata dauka ba. Ana biyu ne ta amsa kiran
"Assalamu alaikum."
Ya amsa da sauri ya k'ara da cewa
"Ina kika shiga inata kira deeya? Ko aljanar ta hau kanki?"
Tayi dariyar maganarsa
"Hum,har yanzu kana yimin kallon aljana kenan?"
Shima dariyar ya danyi
"Ai kece kika kira kanki da aljana kinga kuwa bani da laifi ko? Ina fatan Deeya ta yafewa Yaya j dinta?"
"Sai batun yafiya kakeyi,alhalin ko kusa ni bansan lokacin da kayimin laifi ba yaya j. Laifina ne ba naka ba,ni yafi cancanta na baka hakuri ba kaine yafi dacewa ka bani ba."
Yayi murmushi ya kara gyara zamanshi a cikin motar Haris, wanda ke tuk'i yana sauraronsa.
"Kada ki damu Deeya,donta ni na yafemaki ban rikeki a zuciyata ba kinji?"
Wani sanyin dadi ya mamaye zuciyarta
"Naji yaya j,nagode."
"Yauwa ko kefa deeyata,yaushe zanzo muyi magana?"
Ladi ta ture kwanon tuwonta
"Duk sadda kazo ina maraba dakai."
Yayi murmushi lokacin daya dubi Haris wanda ya tsaya a kofar gidan iyayensa.
"Shikenan deeya,gobe in sha Allah zan shigo."
"Toh yaya j."
Daga haka sukayi sallama.
Haris ya dubeshi yana murmushi
"Menene matsalarka kai kuma?"
Jafar yayi furucin yana harararsa da murmushi dauke akan fuskarsa.
Hakan ya bawa Haris damar tuntsirewa da dariya
"Menene kuwa banda abun boye daya fito fili. Daman na jima ina zargin soyayya kukeyi da wannan kanwartaka. Dole Ibrahim yaji wannan maganar ma don ya tayani dariya. Wato yanzu har gidansu ma ka sani?"
Jafar ya tabe baki hadi da murmusawa
"Kana da aiki fa malam,toh idan ma soyayya mukeyi menene a ciki? Kai karewa ma aurenta nakeson nayi idan Allah Ya yarda."
Haris ya bude baki cikin mamaki
"Wai daman rannan dagaske kakeyi da kace mini kanason kara aure? Wacece wannan data ture gwamnatin Siyama?"
Jafar ya girgiza kansa
"Babu wanda ya isa ya ture gwamnatinta a zuciyana kaji ko? Yauwa,kabar zancen nan ma please. Itama nata bangaren ta samu wanda banyi zaton akwai shi ba a zuciyata."
Haris yayi murmushi
"Ince dai ka taba ganinta kada kaje kaga ba daidai ba."
"Na taba ganinta mana."
Jin Haris zai kara wata tambayar ne ya sanyashi saurin fitowa
"Malam mu shiga mu gaida Hajiya dare yana yi mana."
Haris ya fito yana dariya kafin su shiga.
Hajiya Ummuhani taji dadin zuwansu sosai,ta dubi Jafar
"Daman ana ganinka Jafaru? Ya wajen su Hajja?"
Jafar yana dariya ya amsa mata,yayi mata sannu da dawowa gami da tambayar lafiyar kafarta.
Sun jima har abinci sukaci,kafin tayi musu nasihohi a karshe suka nufi bangaren Alhaji Muniru nan dinma gaisuwa ce da tambayar iyali. Shima ya dora da nashi nasihohin akan tsoron Allah a karshe sukayi musu sallama....
A yanzu Jafar bai fiye takura kansa da damuwar kazantarta ba. Saidai yaja tsaki ya gyara,wataran kuwa Dauda ke taimakonsa.
Ana cikin haka har babbar sallah tazo,ya zauna a dakinsa yayi jugum yana tunani. Fargabarsa bai wuce ya siyo rago ba ya kawo,amma idan Siyama ta soya ya zamana yak'i ciyuwa. Can kuma sai dabara ta fado mishi ya zaro wayarsa ya dannawa Hajja kira. Kara daya biyu ta dauka.
Bayan sallama da gaishe gaishe ne,ya sanar da ita yanason ta turo masa Bahijja saboda aikin nama tunda yasan masu taimakawa Hajjah da sallah suna da yawa. Hajjah tace
"Ba nak'i ayi hakan ba,ni abune na kananun magana banaso. Kayi wa ita Siyamar magana idan ta amince sai a kawota."
Jafar cike da mamaki yace
"Hajiya,Siyama ce zata k'i zuwan Bahijja kuma?"
Hajjah ta danyi shiru,Jafar baisan cewa Siyama ta jima rabonta da cikin gidan nan. Kusan sau hudu tana zuwa gidansu saidai ta bada yaro a kawo mata. Ita kanta batasan abunda ya jawo wannan chanjin ba.
"Hello Hajjah kina jina?"
"Kaidai kayi yanda na gayamaka."
Daga haka ta kashe wayar,ya tsaya sororo yana bin wayar da kallo har Siyama ta shigo goye da Faruk dake bacci.
"Kai kuma lafiya kuwa?"
Ya danyi murmushi
"Hum,barni da Hajja mana,wai nace a turo Bahijja ta taimaka miki da aikace aikacen sallah tace na nemi izninki shine abun yake bani mamaki. Yaushe kuka fara 'yar haka da Bahijjar taki?"
"Kada ki kuskura ki kara barin yar iskar nan ta kara zuwar maki gida. Wani munafuncin ne nasu na daban."
Hudubar da hajiyar ta taba yi mata kenan,nan da nan ta daure fuska
"Menene kuma na neman iznina? Kawai dai Hajja batason turomin ita ne,nikam barshi ma mantawa nayi ban fadamaka ba Hajiya zata aikomin mutum biyu zasu taimakamin. Ba saita zo ba."
Jafar ya mike tsaye,yana zargin wannan chanji na Siyama domin a kwanakin nan rashin kunyarta kara yawaita yakeyi. Baice komai ba har ta fice daga dakin. Ya girgiza kanshi ya mike da niyyar ficewa kasuwa don daman ya kammala shirinsa tsaf.
******
Tun ana gobe sallah,hadiyya suka tafi hutun zuwa kasuwa. Abun yazo mata da dadi saboda anyi musu hutu.
Kwatsam da yamma suna zaune ita da Mama suna lissafin kayan cefane sukaji sallamar Basma. Wani ihun murna Hadiyya ta saki ta rukunkumeta suna dariyar farin cikin ganin juna.
Mama sai murmushi takeyi,ita kanta taji dadin ganin Basma domin tunda ta tafi Zaria, makaranta bata kara zuwa garin ba sai yanzu.
Basma ta saki Hadiyya tayi wajen mama,itama rungumeta tayi tana mai gaisheta. Mama ta rike hannunta tana murmushi mai bayyana hakora
"Yan makaranta,saukar yaushe?"
Basma tana dariya tace
"Dazu dazun nan na iso Mama. Mun sameku lafiya? Ya shirye shiryen sallah?"
"Lafiya kalau mungode Allah. Sallah kam,gatanan ta iskomu sai fatan Allah Yasa muyita lafiya."
Basma tana murmushi ta amsa da amin. Hadiyya ta dubeta
"Taso muje."
Mama ta dakatar da ita ta hanyar harara
"Ni zan fita cefanen? Rike kudin kuje "
Suna dariya suka fice daga gidan bayan Hadiyya ta zura hijabinta a jiki.
A hanya hira kamar suyi me? Hadiyya ta labarta mata yanda take soyewa da Jafar a yanzun,Basma dadi ya rufeta
"Kinga amfanin addu'a Hadiyya. Ga wanda zai gane,ya saki komai ya kama addu a don takobin mumini ce. Nima gashinan da karfin addua mahaifin Bash ya sauko amince da batun aurena dashi. Allah dai Yayi mana jagora."
Hadiyya ta amsa da amin. Sukayita hira har suka isa inda zasuje.
*****
Bayan Sallah da Kwanaki....
Sallamar Shukra da Fatima ta maido da hankalin Siyama daga kallon da takeyi. Ihu ta saki ta rukunkumesu cikin jin dadin ganinsu. Fatima ta tureta saboda nauyin cikin dake jikinta
"Ke taimaka ki matsa so kikeyi nayi haihuwar da ban shirya ba?"
Siyama ta harareta
"Yo idan kin haihu a gidana ai daidai kenan,ko kin mance rabonki da gidana tun bikina?"
Suka zauna Fatima tana yamutsa fuska yayin da take karewa falon kallo
"Siyama fruits kikasha amma baki gyara falon ba?"
Shukra taja tsaki
"Kedai wallahi dama Nazifa aka sanya maki. Haba,ko yaya kikaga datti sai kinyi magana? Siyama bani ruwa idan da abinci ki hado don ko abincin rana banci ba wannan matar ta azazzaleni da waya."
(Shukra da Fatima aminan juna ne kuma kawaye ga Siyama. Tare sukayi karatun firamare zuwa sakandire sun shaku da juna sosai duk da dai akwai bambancin halayya,Fatima duk ta fisu hakuri da sanin ya kamata)
Siyama tace
"Shareta aminiyata,ai Fatima sai a hankali. Wannan da kece uwata bansan ya zanyi ba. Kina fama da jikinki amma baki bar neman rigima ba."
"Atoh dai."
Fatima dai baki ta tab'e
"Ai daman halinku daya baku da bambanci,sai ku koyi hankali yanzu tunda sai an soma tara zuri'a."
Shukra tayi dariya,Siyama dake kicin tana tayata.
"Toh ai tunda muna kyautatawa a shimfida ai inajin magana ta kare ko?"
"Bata kare ba,tsafta da kwalliya da girki suma wani abu ne. Uwa uba ladabi da biyayya."
Siyama wacce ta ajiye faranti cike da nama dayan kuma lemo ne da ruwa tace
"Toh wannan ai mai sauki ne tunda ana kokartawa ko ya kikace aminiyata?😎"
Shukra wacce ta bararraje akan kafet ta gama kwankwadar ruwa tana shirin sanya nama a bakinta ta gyada kai
"Wallahi fa. Bar wannan Nazifar,ita na lura batasan wahalar dake cikin aikace aikace ba tunda su biyu ne wajen mijinta."
Daga haka ta jefa nama a bakinta tana tauna, Fatima tana kokarin shan ruwa,Shukra ta dakatar da ita sakamakon naman data furzo waje .
"Lafiyarki kuwa?"
Shukra tayi saurin bude lemo tasha,sannan ta dubi Siyama
"Allah Ya isa amma,kin kasheni da raina. Wannan wane irin nama ne mai wari haka? Dame kikayi suyarshi? Mts,wallahi Malama yunwa nakeji nikam idan da biredi bani na afa ko zan samu naji daidai."
Siyama ta harareta
"Yau kuma salon wulakancin naki kenan? Wane irin wari a abunda aka soyashi kwanan nan?"
Shukra ta turawa Fatima farantin
"Don Allah ci kiji saiki tabbatar ko sharri nayi gareta. Kema ki dauki kici."
Fatima tunda ta doshi bakinta dashi batayi marmarin kaiwa bakinta ba ta maidashi. Siyama ta tauna ta hau yamutsa fuska
"Oh ni Siyama,a wane roba aka sanyamin naman nan? Ni kaina sai yanzu naji warin. Kodai shiyasa Jafar bayaci?"
Cike da mamaki suka dubeta,Fatima tace
"Amma kin bani kunya,yau kuma mijin naki ne kike kira haka? Ina laifin kiransa da baban faruk? Ta yaya naman nan ma zai ciyu Siyama? Gaskiya baban faruk yana fama."
Haka sukayi mata ca,duk rabin fadan Fatima ke yi,Shukra kuwa biredi da lemo take dank'ara abinta. Idan Fatima ta hado da nata kalar kazantar sai ta hayayyaji tace batasan da wannan ba.
Haka dai a karshe sukayi sallama suka tafi,Siyama bakin cikin lalacewar naman yafi komai nukurkusarta. Ta ja tsaki yafi sau nawa hakanan ta tattara ta ajiye.
******
Watanni biyu da kulluwar soyayyar Jafar da Hadiyya,ya shirya sanarwa iyayensa batun aurensu..
Koya abin xe kasance..?
Nasa mutane xasuce se posting nakeyi..eh sonake inna gudu indena tunoku..!