Hukumar tarihin kwallon kafa duniya ta sanya sunan tsohon dan kwallon Nijeriya, Nwakwo Kanu cikin hazikan 'yan kwallo 48 na duniya.
Da farko hukumar ta fitar da sunayen 'yan wasa kamar su Pelw da Ronaldo da Lima na Brazil.
'Yan kwallon Afrika da suke cikin jerin sunayen sun hada da tsohon dan kwallon duniya, George Oppong Weah, Roger Milla, Rabah Medjer, Muhammed Aboutrika, Mohmud El-Khatub da kuma Lucas Radebe.
Ita dai hukumar an kirkiro ta ne a 1984 a karkashin amincewar hukumar kwallon kafa ta duniya.
Kanu dai da shine dan wasan Nijeriya na baya-baya da ya lashe gasar gwarzon dan kwallon Afrika a 1999.
Ya yi wasa a kungiyoyin Ajax, Inter Milan da Arsenal.
Title :
Kanu Ya shiga Jerin Hazikan 'Yan Kwallon Kafa Na Duniya
Description : Hukumar tarihin kwallon kafa duniya ta sanya sunan tsohon dan kwallon Nijeriya, Nwakwo Kanu cikin hazikan 'yan kwallo 48 na duniya. Da...
Rating :
5