Rahotanni daga garin Jimeta a birnin Yola jihar Adamawa sun nuna cewa wasu jami'an 'yan sanda sun rasa rayukansu sakamakon tashin wani bam hedikwatar hukumar 'yan sanda da ke garin.
Gwamnatin jihar Adamawa dai ta bayar da tabbacin cewa ba harin ta'adanci ba ne, bam din ya tashi ne a matattarar bama-bamai ta 'yan sanda na yankin Jimeta.
Harin ya kuma shafi wata makaranta da ke kusa da ofishin 'yan sandan.
Kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa Ahmad Sajo, ya shaida wa BBC cewa, babu yaron makaranta da ya rasu a lokacin da bam din ya fashe, wasu kalilan ne suka ji rauni, kuma ana
yi musu magani.
Kwamishinan ya kuma ce za su gana da
hukumomin 'yan sanda nan gaba don daukar matakan kaucewa sake faruwar hakan nan gaba.
Title :
Jami'an 'Yan Sanda Sun Rasa Ransu A Yayin Tashin Bam A Hedikwatar 'Yan Sanda A Garin Jimeta
Description : Rahotanni daga garin Jimeta a birnin Yola jihar Adamawa sun nuna cewa wasu jami'an 'yan sanda sun rasa rayukansu sakamakon tashin w...
Rating :
5