DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Wani Mai taimakon Jama'a, mazaunin garin Kaduna mai suna Dr Mahadi Shehu, ya bada tallafin motar kashe gobara da ma'aikatan motar ga jami'ar Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a wajen bayar da tallafin, Dr Mahadi Shehu ya ce babban dalilin daya dauki hankalinshi har ya bada tallafin motar, ya biyo bayan wata munmunan gobara da aka yi a Jami'ar ne a watannin baya, kuma ya duba ya ga babbar jami'a kamar ta Jihar Kaduna ba ta da motar kashe gobara, wannan shine abinda ya zaburar da shi ya sayi sabuwar motar kashe gobarar sannan ya bada ita kyauta ga Jami'ar.
Mahadi Shehu yayi kira da babbar murya ga sauran Jama'a masu hannu da Shuni a fadin Jihar, dasu kasance masu bada tasu gudummuwar ga Jami'ar Jihar, domin a magana ta gaskiya Jami'ar na bukatar dauki.
Lokacin da yake jawabi bayan ya karbi mabudan Motar kashe gobarar, Shugaban Jami'ar ta Jihar Kaduna Farfesa Barnabas Quirix, ya godewa Dr Mahadi Shehu dangane da wannan gagarumar kyauta da yayiwa Jami'ar, inda yayi fatan Allah yayi mishi kyakkyawar sakayya, sannan ya kara yawan ire-irensa a Jihar ta Kaduna.
RARIYA ta zanta da wasu Malamai da Daliban Jami'ar, inda suka bayyana jin dadinsu ga wannan aikin alheri da Dr Mahadi ya yi musu, sannan suka bayyana cewar aiki ne da ya kamata gwamnatin Jihar ta yi tuntuni.
Title :
Jami'ar Jihar Kaduna Ta Samu Tallafin Motar Kashe Gobara
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Wani Mai taimakon Jama'a, mazaunin garin Kaduna mai suna Dr Mahadi Shehu, ya bada tallafin motar kashe gob...
Rating :
5