Shugaba Buhari na Nijeriya ya bayyana cewa yayi dana sanin karbar mulki a wannan lokaci da Nijeriya ke cike da kalubale.
Buhari ya fadi haka ne a London yayin da yake ganawa da 'yan Nijeriya mazauna London.
Buhari ya koka da cewa me yasa yanzu da farashin Fetir ya fadu wanwar daga dalar Amurka 140 zuwa 30 yake karbar mulki? Bayan wadannan kudade ba zasu kawo wa Nijeriya canji da mutane suka zabe shi a kai ba domin ana fama da talauci da bakin jahilci a Nijeriya da ake bukatar makudan kudade don kawo gyara.
Buhari yace a wasu lokuta yana tausayawa talaka ya kuma tausayawa kansa ganin wannan lokaci ba wanda dan Nijeriya zai dara ba don an yiwa Nijeriya karkaf kafin hawansa Mulki.
Buhari ya kuma ce tsarin yin asusun tarayya guda wato TSA ya taimake shi wajen tara fiye da naira tiriliyan 2 yace duk da Jonathan ne ya kawo tsarin to amma shi yayi nasarar tabbatar da tsarin a cewarsa
Title :
Ina Dana Sanni Karbar Mulki Najeriya Wanna Lokaci - Buhari
Description : Shugaba Buhari na Nijeriya ya bayyana cewa yayi dana sanin karbar mulki a wannan lokaci da Nijeriya ke cike da kalubale. Buhari ya fadi hak...
Rating :
5