Muna Bukatar A Kwatar Mana Hakkinmu, Inji Wadanda Wasu Sojoji Guda 7 Suka Yi Wa Dukan-kawo-wuka
Wasu mutane guda biyu mazauna iyakar Abuja da jihar Nassarawa masu suna Injiniya Omashola da Monday Iroka wadanda dukkansu ke zama a gidajen ma'aikatan Dantata da ke unguwar Nyaya-Mararraba, sun aika da wasikar korafinsu ga hukumar kare hakkin dan Adam, sakamakon dukan kawo-wukan da wasu jami'an sojoji suka yi musu, bayan da wani jami'in kare fararen hula ya gayyato su a ranar 16 ga watan Janairu na wannan shekarar.
Mutanen suka ce, rikicin su da jami'in kare fararen hular wanda ke zama a rukunin gidaje na Sani Lulu, ya samo asali ne a ranar 14 ga Janairu a lokacin da ya fasa tayoyin motar wani makwabcinsu, da nufin cewa ya yi gargadin kada a sake ajiye masa mota a kofar gida.
Bincike ya nuna cewa jami'in hukumar kare fararen hular yana aiki ne tare da sojoji a reshen jihar Nassarawa.
Suka ce sakamakon cin zarafin mutane kama daga mata har yara kanana da jami'in kare fararen hular yake yi ne a wannan yankin nasu, sai suka ga ya kamata su kwabe shi. Inda har ta kai ga ya harba bindiga sama da nufin ya razana su.
Mutane biyun suka ce daga bisani sai ga motar sojoji ta shigo unguwar, inda shi kuma mutumin da ya gayyato su mai suna Felix Bamidele ya nuna su ga sojojin, inda suka zuba su a mota suka tafi da su ba tare da jin ta bakinsu ba.
“Bayan mun iso daidai gidan man A.A Rano dake kan titin Keffi da Abuja, sai suka soma jibgar mu. Lamarin ya auku ne da misalin karfe bakwai na yammacin ranar. Kuma sun kai kusan awa daya da rabi suna jibgarmu."
Suka kara da cewa ko ma'aikatan dake gidan man a ranar za su zama shaida kan cin zarafin nasu da sojojin suka yi. Kuma duk wanda ya zo wucewa zai yi zaton wasu 'yan fashi ne aka kama saboda irin yadda aka dinga azabtar da su.
Suka ce babban abin bakin cikin nasu shine, sojojin ba su ma san takamaiman abin da ya hada su da mutumin ba.
Don haka ne suka ga babu inda ya cancanci su kai kukansu kamar hukumar kare hakkin dan Adam din. Wanda a dalilin haka ne ma suka yi kira ga daraktan hukumar, Farfesa Ben Angwe da ya dubi lamarin da idon basira, don ganin an bi musu hakkinsu.
Bincike ya nuna cewar takardar korafin, wadda aka aika ta ga hukumar a ranar 19 ga watan da ya gabata, an kuma aika da kwafenta ga ofishin shugaban rundunar tsaro dake Abuja, amma kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kira su ta lambar wayar da suka sanya a wasikar ba.
Title :
Graphic Photos: Sojojin Najeriya Sun Wasu Mutane Biyu Dukan-Kawo-Wuka
Description : Muna Bukatar A Kwatar Mana Hakkinmu, Inji Wadanda Wasu Sojoji Guda 7 Suka Yi Wa Dukan-kawo-wuka Wasu mutane guda biyu mazauna iyakar Abuja ...
Rating :
5