An bayyana gwamna Nasiru El Rufa'i na jihar Kaduna, a matsayin wani mutum wanda ba ya kaunar 'yan shi'a da tausaya musu.
Bayanin haka yana kunshe ne, a cikin takardar sanarwar da Kungiyar Ci Gaban Mazhabar Ja'afariyya dake da Ofishinta a garin Bauchi, ta rarrabawa manema labarai a Kaduna.
Takardar sanarwar wacce ta samu sanya hannun shugabanta mai suna Abdullahi Hassan, ta bayyana cewar kalaman da Gwamna El Rufa'i ya yi amfani da su, tun da fari dangane da abinda suka kira zaluncin rundunar Sojin Nijeriya akan 'yan Shi'a, kalamai ne wadanda karara suka bayyana rashin adalcin shi, domin tun kafin a je ko'ina El Rufa'i ya karkata gefen sojoji.
Sanarwar ta bayyana cewar bayan zubar da jinin da aka yi, tare da cin zarafin 'yan Shi'a ta hanyar kisa da fyade da aka yi wa matansu da 'ya'yansu, da rurrushe gidaje da wajen ibadarsu da aka yi, gwamnatin El Rufa'i ta kafa wani kwamiti wanda t ace zai binciki dalilin faruwar hakan, amma abin mamaki sai aka sanya gaggan makiyan 'yan Shi'a a cikin kwamitin, wadanda fatansu shine yadda za a shafe 'yan Shi'a daga doron kasa.
Kungiyar ta Ja'afariyyah ta ce ko alama 'ya'yan wannan kwamiti ba su yi ba, saboda babu wakilcin 'yan Shi'a a ciki, sannan babu wani wakili na kungiyar kare hakkin 'yan Adam a ciki na gida kona kasar waje.
Sun bada misali da Farfesa Umar Labdo, wanda suka bayyana shi a matsayin makiyin 'yan Shi'a ta hanyar rubuce rubucen shi, da kuma Farfesa Salihu Shehu wanda suka ce dan' Izala ne.
A ranar Juma'a ne dai gwamna El Rufa'i ya kaddamar da kwamitin mai wakilai 14, inda za su shafe tsawon mako shida suna zama kafin gabatar da rahoton su.
Title :
El Rufa'i Ba YA Tausayin ‘Yan Shi’a - Abdullahi Hassan
Description : An bayyana gwamna Nasiru El Rufa'i na jihar Kaduna, a matsayin wani mutum wanda ba ya kaunar 'yan shi'a da tausaya musu. Bayani...
Rating :
5