*An Kuma Bincike Kan Naira Bilyan 3 Da Aka Gano A Asusun Matarsa
Kimanin dala milyan uku ne hukumar EFCC ta gano a ramin masan gidan tsohon shugaban hafsan sojojin sama, Adesola Amosun, wanda ake kan bincikensa kan kudin sayen makamai, kamar yadda majiyarmu ta jaridar New Telegraph ta rawaito.
Haka kuma majiyar ta kara da cewa ana bin diddigin wasu kudade naira bilyan uku da aka gano a asusun matarsa, Lara Amosu, kamar yadda wata majiya daga hukumar ta EFCC ta shaidawa majiyar ta mu. Sannan kuma majiyar ta kara da cewa matar tsohon shugaban hafsan sojojin saman, tana tsare a hannun hukumar.
Haka kuma a binciken wasu kadarori da hukumar ta yi, ta gano cewa mallakar matar tsohon shugaban hafsan sojojin ne da 'ya'yansa.
Majiyar ta mu ta New Telagraph ta sake bayyana cewa an gano bilyoyin kudade a asusun matar wani hafsan soja wanda yake kula da harkokin kudade na rundunar sojojin saman.
Title :
EFCC Ta Gano Dala Milyan Uku A Ramin Masan Gidan Tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Sama
Description : *An Kuma Bincike Kan Naira Bilyan 3 Da Aka Gano A Asusun Matarsa Kimanin dala milyan uku ne hukumar EFCC ta gano a ramin masan gidan tsoho...
Rating :
5