Hukumar EFCC ta cafke wani babban hafsan sojojin saman Nijeriya wanda ake zargin yana daga cikin wadanda suka ci dala bilyan 2.1 na kudin makamai.
Bincike ya nuna cewa hafsan sojojin mai suna AVM R.A Ojuowo, an kama shi ne a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe dake Abuja, a lokacin da yake shirin barin kasar a cikin makon nan.
Majiyarmu ta kara da cewa an kama Ojuwo ne a yayin da ya raka shugaban hafsan hafsoshin sojoji Janar Gabriel Olonisakin, domin halartar taro kan harkar tsaron na kungiyar hadin kan kasashen Afrika wanda za a gudanar a kasar Jamus a ranar Lahadi mai zuwa.
Haka kuma duk da magiyar da tawagar sojojin da za su haura kasashen wajen suka yi wa hukumar ta EFCC domin ganin sun bari Ojuwo ya halarci taron, kafin daga bisani ya gufanar da kansa a gaban hukumar, amma sun yi kememe. Inda suka tallafo keyarsa domin gudanar da bincike akansa.
Hafsan sojan yana daya daga cikin manyan hafsojin sojojin da hukumar EFCC ta gayyata domin tuhumar su kan kudin sayen makamai.
Title :
EFCC Ta Cafke Wani Hafsan Soja A Hanyarsa Ta Ketarawa Kasar Waje
Description : Hukumar EFCC ta cafke wani babban hafsan sojojin saman Nijeriya wanda ake zargin yana daga cikin wadanda suka ci dala bilyan 2.1 na kudin m...
Rating :
5