Hukumar EFCC a ranar Talatar da ta gabata ta maka wani mai suna Sabo Sani Labaran a babban kotun jihar Gombe karkashin jagorancin mai shari'a Abubakar Jauro, bisa zarginsa da aikata laifuka biyu wadanda suka haka da sojan gona da kuma damfara, inda ya karbi sama da naira dubu 242.
Wanda ake zargin, wanda ya kware a fannin damfara ta yanar gizo, a cikin watan Oktoban da ya gabata ya karbi kudi har naira dubu 242 a wurin wani mai suna Alhaji Hussaini Mai Magani, inda ya yi masa alkawarin cewa zai ba shi kwangilar odar kayan asibiti.
Daga bisani wanda ake zargin, wanda yake amsa sunan gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo a shafinsa na facebook, ya karkatar da kudin domin biyan bukatun kansa.
Wanda ake tuhumar ya musanta zargin da ake yi masa a kotu. Wanda a sakamakon haka lauya mai kare shi, Rahimat I. Talle ta nemi kotun da ta bada belinsa
Daga bisani dai kotu ta sanya ranar 8 ga watan da muke ci a matsayin ranar ci gaba da sauraren shari'ar. Inda kuma ta bada umarnin a ci gaba da tsare shi.
Title :
Dubun Wani Mai Damfara Da Sunan Gwamnan Jihar Gombe Ya Cika
Description : Hukumar EFCC a ranar Talatar da ta gabata ta maka wani mai suna Sabo Sani Labaran a babban kotun jihar Gombe karkashin jagorancin mai shari...
Rating :
5