DARAJAR NAIRA TA FARA FARFADOWA, YAU DALLAR AMURKA DAYA NA DAIDAI DA NAIRA 305
Sakamakon turjiya da shugaban qasa yayi na ya rage darajar Naira da kuma maida hankali wajen sarrafa kayan buqatun yau da kullum a gida. Sai gashi buqatar Dallar Amurka ta fara raguwa a Nigeria. Qarancin buqatar dallar ya haifar da farfadowar darajar Naira a kwana biyu da suka wuce.
Idan baku manta ba, Naira ta fadi warwas a makon jiya inda Dallar Amurka daya ta kai Naira 390. Wannan yasa masu hasashe kintatan cewa lallai bada dadewa ba za a siya Dallar har Naira 400. Amma faduwar Dallar ya sanya jama'a sun sami qarfin gwuiwar cewa lallai darajar Naira na nan dawowa bada dadewa ba.
Ko ma dai manene, muna kira da 'yan Nigeria da su taimaka wajen dawo da darajar Naira ta wurin rage amfani da kayan waje kamar kayan gwanjo da kayan abinci. Hakan zai sake rage buqatar kudaden qasar waje kuma zai habbaka tattalin arzikinmu.
Title :
Daraja Naira Ta Fara Farfadowa
Description : DARAJAR NAIRA TA FARA FARFADOWA, YAU DALLAR AMURKA DAYA NA DAIDAI DA NAIRA 305 Sakamakon turjiya da shugaban qasa yayi na ya rage darajar ...
Rating :
5