Rahotanni daga jihar Gombe na bayani da cewa wani dalibin makarantar sakandaren gwamanati ya rasa ransa a sanadiyar harbinsa da wani jami'in ‘yan Sanda yayi a filin wasa na unguwar Fantami dake cikin garin Gombe.
Hukumar makarantar da dalibin yake tace bayan da aka tashi daga wasa ne lamarin ya faru, dalibin mai suna Sadiq Yunusa, yana zangon karshe ne na kammala karatunsa a matakin zuwa Jami'a.
Mataimakiyar shugaban makarantar da aka kashe dalibin Malama Zahara Yahaya, tace abinda ya faru shine yara sunje filin wasa domin suyi wasa bayan da aka gama wasa, sai aka fara jifa wanda yara ‘yan makaranta kan yi a junansu, ‘dan Sandan na tsaye jifa ya sameshi a kai ba tare da sanin ta inda jifan ya fito ba.
Dan Sandan yayi fushi ya son ya rama, wani Malami dake gurin ya bashi hakuri amma bai hakura ba, Sadiq ya nufi motar makaranta da ta kai su domin tafiya gida, sai ‘dan Sandan ya dauki bindigarsa ya harbe shi a ka, nan take Sadiq ya rasa ransa.
Mallamin dake koyar da darusan wasanni a makarantar Mallam Kalif Isiyaku, yayiwa wakilin Muryar Amurka karin haske kan wannan lamari. Inda yace irin wannan jifa an saba gani yara nayi ba wani sabon abu bane, duk da yake an baiwa ‘dan Sandan hakuri amma yaki ji har ya bude wuta kan ‘dalibi wanda baya dauke da komai.
Kakakin yan Sandan jihar Gombe, DSP Faji Attajiri, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace ana gudanar da bincike.
Title :
Dan Sanda Ya Bindige Wani Dalibi Har Lahira A Gombe
Description : Rahotanni daga jihar Gombe na bayani da cewa wani dalibin makarantar sakandaren gwamanati ya rasa ransa a sanadiyar harbinsa da wani jami...
Rating :
5