Tsohon jakadan Nijeriya a kasar Burtaniya, Sanata Dalhatu Sarki Tafida, ya ce ya yanke shawarar barin jam'iyyar PDP ne saboda a cewar sa ta rasa alkibla.
Ya kara da cewa a yanzu babu wani aiki da PDP ta ke yi, a da can dai sun yi abin azo a gani amma yanzu sai kwaso mutanen da bai dace ba jam'iyyar ke yi.
Ya kuma ce jam'iyyar PDP ba ta bai wa mutane irinsa girma, ba kuma a daukar shawarar su sai dai abinda 'ya'yan jam'iyyar suka ga damar yi.
Sanata Tafida ya ce kawo yanzu bai shiga kowacce jam'iyya ba, ya na dai yin nazari dan sanin inda ya dace ya nufa.
Title :
Dalilin Da Ya Sa Na Bar PDP - Dalhatu Sarki Tafida
Description : Tsohon jakadan Nijeriya a kasar Burtaniya, Sanata Dalhatu Sarki Tafida, ya ce ya yanke shawarar barin jam'iyyar PDP ne saboda a cewar s...
Rating :
5