Ya Ce Yana Da Dalilai Kan Yadda Musulmai Suka Fi Yin Imani Da Annabi Isa (A.S) Fiye Da Mabiya Addinin Kirista:
Ga Dalilan Nasa;
1. Annabi (Jesus) ya bayyana cewa Allah daya ne, kuma shi kadai ne abin bauta, kamar yadda ya zo a littafin bible (Deut 6:4, Mark 12:29). Su ma Musulmai sun yi imani da hakan a Alkur’ani (4:171).
2. Annabi Isah A.S, ba ya cin alade, kamar yadda ya zo a bible (Leviticus 11:7), kamar yadda su ma Musulmai ya zo musu a Alkur’ani (sura ta 6:145).
3. Annabi Isa ya kan yi amfani da Kalmar "As-salaam alaikum" wajen gaida mutane (John 20:21), kamar yadda su ma Musulmai suke yi.
4. Annabi (Jesus) yana amfani da kalmar da yardar Allah (InshAllah), kamar yadda su Musulmai suke yi a duk al’amuran da za su yi (Alkur’ani 18:23-24).
5. Annabi Isa (Jesus) yakan yi alwala kafin ya gudanar da ibada, kamar yadda Musulmai suke yi.
6. Annabi Isa (Jesus) da sauran Annabawa da aka ambaci sunansu a littafin Bible suna yin sujjada ne a yayin da suke ibada, kamar yadda ya zo a (Matthew 26:39). Kuma su ma Musulmai haka suke yi (Qur'an sura ta 3:43.
7. Annabi Isa ya bar gemu, wadda ita ma dabi’a ce ta Musulmai.
8. Annabi Isah ya yi imani da dukkanin Annabawa kamar yadda ya zo a (Matthew 5:17). Su ma kuma Musulmai sun yi imani da Annabawa kamar yadda ya zo a (Qur'an sura ta 3:84, da 2:285.
9.Mahaifiyar Annabi Isa, Nana Maryam, ta kan rufe jikinta da wadatattun kaya tare da sanya hijabi kamar yadda ya zo a surori daban daban a bible (Timothy 2:9, Genesis 24:64-65, da Corinthians 11:6). Haka su ma matan Musulmai irin shigar da suke yi kenan kamar yadda yake a Alkur’ani sura ta 33:59.
10. Annabi Isah da sauran Annabawan da aka ambanci sunansu a Bible sun yi zumi na sama da kwanaki 40, ku duba (Exodus 34:28, Daniel 10:2-6, 1 Kings 19:8, da Matthew 4:1.
Sai ga shi su ma Musulmai an umarce su da azumtar kwanaki talatin na watan Ramadan. (Ku duba Qur'an 2:183), baya ga haka kuma wasu sukan yi azumin kwanaki shidda, wato sitta Shawwal bayan Ramadan.
11. Annabi Isa ya kan yi sallama idan zai shiga gida, kamar yadda ya zo a bible (Luke 10:5, sannan kuma ya kan yi wa jama’ar da ya tarar a gidan sallama. Haka su ma Musulmai suna yin daidai yadda ya yi, kamar yadda ya zo a Kur’ani (24;61).
Yanzu sai a fada min wanene cikakken mai bin Annabi Isa tsakanin Musulmi Da Kirista? Yanzu na yi imani cewa ina kan addinin gaskiya, Inji Emmanuel Adebayo, wanda ya buga wasa a kungiyoyi irin su Real Madrid, Arsenal, Monaco, Man City da sauransu.
Title :
Dalilan Da Suka Sa Na Musulunta - Emmanuel Adebayo
Description : Ya Ce Yana Da Dalilai Kan Yadda Musulmai Suka Fi Yin Imani Da Annabi Isa (A.S) Fiye Da Mabiya Addinin Kirista: Ga Dalilan Nasa; 1. Annabi...
Rating :
5