A yau Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasashen Burtaniya da Faransa.
A tsayawar farko da zai yi a garin Strasbourg a Faransa, shugaba Buhari a gobe Laraba zai gabatar da jawabi a taron kungiyar Turai.
Jawabin shugaban kasar kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana, zai mayar da hankali ne kan al'amuran ta'addanci, cin hanci da rashawa da kuma matsalar rashin tsaro da Nijeriya da ma sauran kasashen Afrika ke fama da su. Don ganin sun samu tallafi daga kungiyar ta Turai.
Haka kuma shugaba Buhari zai gana da shugaban kungiyar, Mista Martin Schlz da sauran shugabanni kungiyar kan matsalolin da ya gabatar, kafin daga bisani ya kara gaba zuwa birnin Landan domin halartar taro kan goyon bayan kasar Syria wanda za a gudanar a ranar Alhamis.
A nan bangaren kuma, Buhari zai yi amfani da damar wannan taro, wanda kasahe irin su Jamus, Burtaniya, Norway, Kuwait, Majalisar Dinkin Duniya da sauransu suka dauki nauyi, wajen samun goyon bayan kasashen don ganin an yaki ta'addanci a Nijeriya da ma sauran kasashen yankin Afrika.
Ana tsammanin Buhari zai dawo Nijeriya ne a karshen makon nan.
Title :
Buhari Zai Ziyarci Kasashen Burtaniya Da Faransa
Description : A yau Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasashen Burtaniya da Faransa. A tsayawar farko da zai yi a garin Strasbourg a Faran...
Rating :
5