Daga Sani Musa
Gwanatin jihar Nasarawa ta ce nan ba da dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude babbar kasuwa ta kasa da kasa dake Karu, wadda ke makwabtaka da Babban birnin taraiya Abuja.
Gwanan jahar Alhaji Umar Tanko Almakura ne ya bayyana hakan bayan kammala rangadin kasuwar da wasu ayukan hanyoyin da gwanatin jihar ke yi a yankin Mararaba.
Alhaji Tanko Almakura ya ce idan an bude kasuwar mai shaguna fiye da dubu biyar, duk kananan 'yan kasuwa masu sayar da hajoji a gefen tagwayen hanyoyin Abuja zuwa keffi za su koma cikin ta, wanda a cewar sa hakan zai rage cin koson ababan hawa da ake fama da su akan hanyoyin, musamma daga Mararaba zuwa Nyanya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jama'a da su gujewa zubar da shara barkatai a bisa hanyoyi. Ya ce an samar da wuraren zubar da shara wanda hukumar raya birnanai ta jihar Nasarawa take kwashe wa idan sharar ta cika.
Jama'a da dama da dai sun bayyana jin dadin su da wannan furuci na gwanan. Sun ce bude kasuwar wadda aka fara ginawa tun a shekara ta 2002, zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Nasarawa.
Title :
Buhari Zai Jagoranci Bude Sabuwar Kasuwar Kasa Da Kasa Ta Karu
Description : Daga Sani Musa Gwanatin jihar Nasarawa ta ce nan ba da dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude babbar kasuwa ta kasa da kasa dak...
Rating :
5