Gwamnatin tarayya ta sallami shugabannin kafofin yada labarai mallakinta guda shida.
Wata sanarwa da Mista Segun Adeyemi, kakakin ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar a yau Litininta, ta ce an kori shugabannin gidan talabijin na gwamnatin tarayya, (NTA), da Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN), da muryar Najeriya, da kamfanin dillacin labarai na kasar (NAN), da hukumar sa idanu a kan kafafen watsa labarai na kasar da hukumar wayar da kan jama'a ta kasar (NOA).
Ministan ya bai wa shugabannin da aka sallama umarnin mika al'amuran hukumomin nasu ga manyan jami'an gwamnati da ke ma'aikatun.
Title :
Buhari Ya Sallami Shugabannin Kafafun Yada Labarai Na NTA, FRCN, NAN Da Sauransu
Description : Gwamnatin tarayya ta sallami shugabannin kafofin yada labarai mallakinta guda shida. Wata sanarwa da Mista Segun Adeyemi, kakakin ministan...
Rating :
5