Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jimaminsa game da rasuwar Hajiya Fati Koko wadda aka fi sani da Maitalle Tara, wadda ta rasu tana da shekaru 95.
Idan ba a mance ba, marigayiya Hajiya Koko ta yi zaman jiran zuwan Buhari garin Kebbi har na tsawon awanni tara a yayin da yake yakin neman zabe, inda har ta ba shi gudummawar naira milya daya.
A jawabin da shugaba Buhari ya fitar ta bakin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kyakkyawar zuciya wadda a koda yaushe take tare da gaskiya.
Marigayiyar ta tallafawa Buhari da adadin wadannan kudaden da ta tara ne a sana'ar sayar da tuwo da take yi, inda ta ce ta yi hakan ne saboda girmama shugaban kasar da take yi wajen gaskiya da rikon amanarsa.
A yayin da labarin rasuwarta ya iso ga shugaban kasar, ya bayyana ta a matsayin mutuniyar kirki wacce ya kamata al'umma su yi koyi da ita.
"Ta bada gudummawar dukkan dukiyar da ta mallaka a yayin yakin neman zaben da muka yi. Duk da irin yawan shekarun da take da su, amma hakan bai hana ta neman canjin a kasar nan ba. Don haka rayuwarta a bar koyi ce ga al'ummar Nijeriya.
Buhari ya kuma mika ta'aziyyar rasuwarta ga iyalanta.
Haka kuma Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu da sauran al'ummar jihar Kebbi wadanda ya ce za su yi rashin duk wasu kyawawan dabi'u na Hajiya Koko.
"Allah ya yi mata rahma", kamar yadda Buhari ya ce.
Title :
Buhari Ya Nuna Jimaminsa Kan Rasuwar Hajiya Fati Koko
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jimaminsa game da rasuwar Hajiya Fati Koko wadda aka fi sani da Maitalle Tara, wadda ta rasu tana da...
Rating :
5