Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose jiya ya bayyana cewa akwai matsala a kasar nan kuma shi ne Allah ya horewa wani sirri da zai fallasa kafin matsalar ta gagara.
Fayose ya fadi haka ne a garin Fatakwal ta jihar Rivers wajen taron godiya ga ubangiji kan nasarar da gwamna Wike ya samu a kotun koli.
Fayose yace sirrin da Allah ya ganar da shi, shine, Buhari da wasu gwamnoninsa 5 da wasu sarakunan gargajiya na shirin musluntar da Nijeriya a boye daga kasar Saudia.
Fayose yace ba a isa ba,kuma dole a tafi yadda aka taso wato can a kira Sunan "Allah" a can kuma a kira "Jesus", kuma duk wani chanji da APC ke kokarin kawo sabanin haka zai gamu da tirjiya daga gun su.
Fayose daga karshe yayi wa mahalarta wannan taro albishir din cewa PDP zata dawo mulki a 2019 ganin yadda Buhari ya kasa dai dai tattalin arzikin Nijeriya kamar yadda yayi wa talaka alƘawari.
Title :
Buhari Ya Naso Yadawo Da Najeriya Kasar Musulunci A Munafurce - Fayose
Description : Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose jiya ya bayyana cewa akwai matsala a kasar nan kuma shi ne Allah ya horewa wani sirri da zai fallasa kafi...
Rating :
5