Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani makaho mai suna Samuel Inalegwu Ode Ankeli a matsayin babban mai taimaka masa.
Babban mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, shi ya bayyana hakan a yau, inda ya ce Ankeli shi zai taimakawa Buhari wajen mu'amala da nakasassu.
Garba Shehu ya kara da cewa, Ankeli shi ya jagoranci kungiyar nakasassu magoya bayan Buhari/Osinbajo zuwa hedikwatar APC ta kasa, inda wannan shine karo na farko da aka yi wa wata jam'iyyar haka a tarihin kasar nan.
Sannan kuma ya kara da cewa hankali ya kuma ja hankulan nakasassun wajen ganin sun marawa Buhari da Osinbajo baya a zaben 2015.
Mutumin dai dan asalin jihar Benue ne. Ya halarci wata makaranta a garin Giwa dake kusa da Zaria, kafin daga bisani ya karancin harkar magungunan dabbobi a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.