Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun ce wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kaddamar da hare-haren a wasu kauyuka da ke kusa da Maiduguri.
Bayanai sun ce mayakan sun halaka mutane hudu a hare- haren da suka kai a kauyukan Malari da kuma Mairi masu tazarar kilomita 20 daga Maiduguri.
Wani mazaunin kauyen Mairi ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kai hare-haren ne a ranar Juma'a da yamma inda suka kona gidaje da dabbobi masu yawa. Wannan harin shi ne na baya-bayanan da 'yan Boko Haram suka kai a daidai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da ikirarin samun galaba a kan kungiyar.
Title :
Boko Haram Ta Kai Wani Sabo Hari A Kauyen Maiduguri
Description : Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun ce wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kaddamar da hare-haren a wasu kauyuka da ke kusa ...
Rating :
5