Kimanin mutane talatin ne suka rasa ransu a wasu hare hare da 'yan Boko Haram suka kai a karshen makon nan, a wasu kauyuka biyu dake karamar hukumar Damboa a jihar Borno, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigan sun budewa jama'a wuta ne a yayin da suka kira su zuwa wani masallaci dake kauyen Yakshari a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe mutane 22, bayan wani hari da suka kaiwa wasu matafiya da suke ka hanyar shigowa kauyensu, inda nan ma suka kashe mutane takwas.
Wani ganau ba jiyau ba, mai suna Buni Saje ya bayyana cewa wasu da dama sun samu rauni a harin na Yakshari kuma an garzaya da su asibitin garin Biu. Haka kuma 'yan bindigan sun yi awon gaba da mata uku, tare da kwashe dabbobi, kayan abinci da sauransu, inda suka kwashi kayan a motoci biyun da suka kwata a kauyen. Sannan kuma sun kona wasu motoci biyu da basu tashi.
Title :
Boko Haram Sun Kashe Mutane Talatin A Jihar Borno
Description : Kimanin mutane talatin ne suka rasa ransu a wasu hare hare da 'yan Boko Haram suka kai a karshen makon nan, a wasu kauyuka biyu dake ka...
Rating :
5